‘Za mu yi amfani da masu unguwanni domin samar da tsaro a Rigasa’

Shugaban Riko na karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, Dokta Ibrahim Yusha’u ya ce majalisarsa da gwamnatin jihar za su yi amfani da masu unguwanni da dagatai da sarakunan gargajiya wajen tabbatar da tsaro a garin Rigasa. Garin Rigasa da ke kusa da Kaduna ya yi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci da matasa ke yin […]

‘Za mu yi amfani da masu unguwanni domin samar da tsaro a Rigasa’
‘Za mu yi amfani da masu unguwanni domin samar da tsaro a Rigasa’

Shugaban Riko na karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, Dokta Ibrahim Yusha’u ya ce majalisarsa da gwamnatin jihar za su yi amfani da masu unguwanni da dagatai da sarakunan gargajiya wajen tabbatar da tsaro a garin Rigasa.
Garin Rigasa da ke kusa da Kaduna ya yi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci da matasa ke yin sara-suka, wanda hakan ya sa sabon shugaban ya ce sun lashe takobin kawo karshen wannan matsala a yankin.
Dokta Ibrahim Yusha’u ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da wata kungiyar matasa a yankin mai suna Albarka Youth Forum ta shirya domin ta ya shi murnar samun wannan matsayi.Shugaban ya ce tun lokacin da Gwamna Nasir El-Rufa’i ya hau kan mulki, ya dukufa wajen ganin an magance ayyukan ta’adda da barna ba a yankin Rigasa kadai ba har ma da jihar baki daya.
Ya ce batun tsaro ne babban matakin da gwamnatin El-Rufai za ta sa a gaba a jihar. “Domin idan aka ce babu dauwamammen zaman lafiya, to sauran abubuwa ba za sa samun wurin zama ba, ko da kuwa addini ne. Hakika wannan gwamnati, tun daga matakin unguwanni zuwa karamar hukuma da jiha baki daya, ta yi kyakkyawan tanadi don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Wannan ne ya sa za mu yi aiki kafada-da-kafada da masu unguwanni da sarakuna da mukarrabansu da kungiyoyi da sauran al’umma wajen ganin gwamnati ta cimma wannan buri nata. Muna tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi don ganin an magance kaurin sunan da wannan unguwa ta yi wajen rikici da tashe-tashen hankula. Kuma za mu bude ofisoshin ’yan sanda a wurare uku a karamar Hukumar Igabi, kuma lallai Rigasa tana nan tafe, in Allah Ya so abin zai tabbata.”
Sai ya yi kira ga jama’ar yankin su ba gwamnatin jihar goyon baya domin kawo karshen matsalarrashin tsaro a yankin Rigasa da jihar baki daya.
Ya ce kowane mutum yana da gudunmawar da zai bayar, wajen sa ido da kai rahoton duk wanda suke shakkar harkokinsa ga hukuma.
Ya yi godiya ga kungiyar kan shirya wannan taro inda ya ce zai yi iyakar kokarinsa a matsayinsa na mutum na farko daga yankin Rigasa da zai rike shugabancin karamar hukumar wajen kawo ci gaba a yankin.
Kakakin kungiyar Malam Rilwanu Abdullahi ya mika godiyarsu ga Gwamna Nasir El-Rufa’i bisa nada dan garin Rigasa a matsayin shugaban karamar hukumar.