Za mu yi maganin duk mai tayar da hankali a Kudancin Kaduna – Janar Nicholas

  Kwamandan Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya a Jihar Filato (OPSH), wanda aka hada masa da kananan hukumomi hudu na Kudancin Jihar Kaduna da suka hada da Sanga da Jama’a da Kaura da Zangon Kataf, Manjo Janar Rochas I. Nicholas, ya ce a shirye rundunarsa take ta yi maganin duk wani marar ji da ya kuskura […]

Za mu yi maganin duk mai tayar da hankali a Kudancin Kaduna – Janar Nicholas
Za mu yi maganin duk mai tayar da hankali a Kudancin Kaduna – Janar Nicholas

 

Kwamandan Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya a Jihar Filato (OPSH), wanda aka hada masa da kananan hukumomi hudu na Kudancin Jihar Kaduna da suka hada da Sanga da Jama’a da Kaura da Zangon Kataf, Manjo Janar Rochas I. Nicholas, ya ce a shirye rundunarsa take ta yi maganin duk wani marar ji da ya kuskura ya sake takala ko kuma yunkurin sake haddasa wata fitina a yankin Kudancin Kaduna.

Manjo Janar Rochas I. Nicholas wanda ya bayyana haka a wurin wani taro da aka shirya kan ci gaba da nemo mafita game da rikice-rikicen Kudancin Kaduna da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a dakin taro na otel din New Choice da ke garin Kafanchan, ya ce babban abin da ya kawo su wannan yankin shi ne samar da zaman lafiya ba maganar siyasa ba.

Janar Nicholas ya kuma ce dole ne a bude dukanin labin shanu da Fulani suke bi da aka san da su tuntuni, wadanda manoma suka toshe. Kuma duk wanda ya kuskura ya sake taba wani Bafulatani ko dabbobinsu a kan hanyar bin wadannan labi to rundunarsa za ta yi maganinsa.

Kwamandan ya kuma yi kira ga Fulani makiyaya su daina tura kananan yara da ba su gama mallakar hankalinsu ba zuwa kiwo, kuma da zarar yamma ta yi su kora dabbobinsu zuwa gida domin “Duk wanda muka sake ganinsa yana kiwo da daddare za mu harbe shi,” inji shi.

A karshe ya yi kira ga makiyaya da manoma su kiyaye hakkokin juna kuma duk lokacin da makiyayi ya barnata kayan gona ko kuma manomi ya shiga hakkin makiyayi ta hanyar toshe masa hanyar kiwonsa, to su yi gaggawar sanar da su domin daukar matakin da ya dace ba tare da wani ya dauki doka a hannunsa ba.

Kwamandan ya kuma tabo batun cewa duk sojan da ya tsare wani direba ko mai tuka babur to a ba su hadin kai domin aikinsu bincike ne kawai amma duk lokacin da wani soja ya bukaci a ba shi na goro to wannan ya saba doka kuma a yi maza a sanar da su don hukunta shi. Domin kuwa, kamar yadda ya ce, suna ba su duk wani alawus da sauran hakkokin da suka dace.

Dukanin masu gabatar da jawabi da suka hada da Rabaran Para Mallam da Bishop Markus da Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Kafanchan, Alhaji Muhammad Kabir Kasim, sun yi kira ga mahalarta taron kan irin muhimmancin da zaman lafiya ke da shi da kuma hanyoyin da za a bi domin samun ci gaba da wanzuwar zaman lafiya.

A jawabin, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Jama’a da Sanga, Mista Garba Shehu (Sarkin Noma), ya bayyana cewa bisa ga irin kewayen jin ra’ayin jama’a da ya yi, ya fahimci babu abin da kowa ke so yanzu sai zaman lafiya. Sai ya yi kira da kowa ya yi kokarin yin aiki, tare da isar da sakon zaman lafiya ga jama’arsa, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su rika yin gaggawar daukar mataki a duk lokacin da aka sanar da su faruwar wani abu a wani wuri.