Za mu yi murabus idan gwamnati ta rage mana albashi- Kwamishinonin Nasarawa

Kwashinonin Jihar Nasarawa sun ce a shirye suke su yi murabus daga mukamansu muddin Gwamnan Jihar, Umaru Tanko Al-Makura ya aiwatar da shirinsa na rage kashi 30 daga cikin albashinsu. daya daga cikin kwamishinonin da wakilinmu ya tattauna da shi a ma’aikatarsa a Lafiya da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce tuni galibinsu suka […]

Za mu yi murabus idan gwamnati ta rage mana albashi- Kwamishinonin Nasarawa
Za mu yi murabus idan gwamnati ta rage mana albashi- Kwamishinonin Nasarawa

Kwashinonin Jihar Nasarawa sun ce a shirye suke su yi murabus daga mukamansu muddin Gwamnan Jihar, Umaru Tanko Al-Makura ya aiwatar da shirinsa na rage kashi 30 daga cikin albashinsu.
daya daga cikin kwamishinonin da wakilinmu ya tattauna da shi a ma’aikatarsa a Lafiya da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce tuni galibinsu suka yi zama a kan batun, inda suka yanke shawarar yin murabus da zarar gwamnatin jihar ta aiwatar da wannan shiri. Ya ce “Game da batun rage mana kashi 30 daga cikin albashinmu da gwamnati ta sanar kwanan nan kuma take shirin aiwatarwa, ina so in sanar da kai cewa ba za mu amince da haka ba. Domin kamar yadda ka sani yanzu babu kudin nan da ake kira na gudanar da ayyuka (Oberhead) a asusun ma’aikatunmu kuma ga jama’a sun yi mana yawa, kullum idan sun zo ofishinka za ka biya musu bukatu ga kuma bukatun ma’aikatanmu da sauransu. Duk wadannan hidimomi muna yi ne daga albashinmu wanda ba ya ma isarmu mu kashe zuwa wani watan. Duk da haka sai a ce za a rage kashi 30 daga ciki. Idan aka yi haka nawa ne zai rage mana mu biya bukatunmu da na jama’a.”
Kwamsihinan ya kara da cewa: “Ina so in sanar maka cewa galibinmu suna ne kawai muke amsawa a matsayin kwamishinoni a jihar nan, amma ba ma iya cimma hidimomin kwamishina. Shi ya sa muka yi zama na gaggawa da muka ji wannan shiri na gwamnati, inda muka ce gara mu ’yar da kwallon mangwaro mu rabu da kuda ta hanyar yin murabus daga mukamanmu da zarar gwamnati ta aiwatar da wannan shiri maimakon jama’a su ci gaba da zarginmu ba gaira ba dalili.”
Daga nan sai ya yi amfani da damar, inda ya shawarci gwamnatin jihar ta rage burinta na ci gaba da gudanar da manyan ayyuka maimakon haka ta kammala wadanda ta faro ta kuma fadada hanyoyin samun kudin shiga ga jihar don cimma bukatun jihar maimakon rage albashin ma’aikata da ya ce bai taka kara ya karya ba a kuma wannan mawuyacin hali.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya sanar a jawabinsa jim kadan bayan ya sanya hannu a kasafin kudin bana cewa shi da mataimakinsa za su rika karbar rabin albashinsu ne, inda ya ce za a kuma rage kashi 30 cikin 100 daga albashin kwamishinonin domin bai wa gwamnatinsa damar ci gaba da samar wa al’ummar jihar ribar dimokuradiyya, zuwa lokacin da tattalin arzikin jihar zai inganta.