Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

Doguwa, ya ce akwai buƙatar Kwankwaso ya nemi mafita a siyasa kafin zaɓen 2027.

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudunwada, Alhassan Ado Doguwa, ya mayar da martani kan furucin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi cewa ’yan Najeriya za su kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Kwankwaso, a lokacin da yake jawabi a wani taron siyasa a Kano, ya ce ’yan Najeriya, musamman ma ’yan Arewa, sun gaji da APC kuma za su sauya ta a zaɓen 2027.

Doguwa, ya ce Kwankwaso har yanzu bai farfaɗo daga kayen da ya sha a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023 ba.

Ya shawarci Kwankwaso ya daina mafarki ya fara neman mafita game da siyasarsa kafin zaɓen 2027.

“A bayyana yake cewar Kwankwaso bai gama warkewa daga shan kaye da ya yi a 2023 a hannun Shugaba Tinubu ba. Furucinsa na cewa ‘yan Najeriya sun gaji da APC ba komai ba ne face mafarki. Ya kamata ya nemi mafita kafin zaɓen 2027,” in ji Doguwa.

Doguwa, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur, ya ce kalaman Kwankwaso ba su da ma’ana.

“A wani taron siyasa, Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa za a sauya APC a 2027. Lokaci ya yi da zai daina mafarki kuma ya amince cewa lokacinsa a siyasa yana gab da ƙarewa.”

Doguwa ya ƙara da cewa Tinubu yana aiki tuƙuru wajen gyara tattalin arz5ikin ƙasar da inganta al’amura.

Ya kuma bayyana cewa, ƙarƙashin jagorancin Tinubu, Najeriya ta jawo hankalin masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje da suka kai Dala biliyan 30 cikin watanni 16, kuma an rage bashin ƙasar tare da ƙara kuɗaɗen shiga.

Ya kuma bayyana ci gaban da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce gwamnati ta kashe manyan kwamandojin Boko Haram.

Kazalika, ya ce an kashe manyan ‘yan fashin daji sama da 300, ciki har da Kachalla Halilu Sububu, wanda ya addabi Sakkwato, Zamfara, Katsina da kuma Kaduna.

Doguwa ya bayyana cewa ya na da yaƙinin cewa matsalolin da ake fuskanta a ƙasar za su ragu nan ba da jimawa ba, yayin da matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka za su fara bayar da sakamako mai kyau.

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom