Za mu zakulo wadanda suka kashe jami’anmu a Delta — ’Yan sanda
Baya ga cewa [kisa] zunubi ne da rashin mutuntawa, haka kuma dukkan addinai sun haramta yin hakan.
Hukumomin ’yan sandan Najeriya sun sha alwashin yin amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen zaƙulo waɗanda suka kashe jami’an tsaro a kwanan baya a Jihar Delta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar (FPRO), ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV a cikin shirin Siyasa a Yau.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da ganawa da manyan hafsoshi da kuma mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu domin daukar matakan da suka dace game da matsalar tsaro a yankin Neja Delta.
- Ana neman mutane 8 ruwa a jallo kan kisan sojoji a Delta
- An miƙa wa sojoji Sarkin da ake nema ruwa a jallo kan kisan dakaru a Delta
Adejobi ya ce babu ɗaya daga cikin waɗanda suka kashe jami’an tsaro a Jihar Delta da ba zai fuskanci hukunci ba domin rundunar na samun muhimman bayanai kan waɗanda ake zargi gaba ɗaya.
Ya ci gaba da cewa, “Baya ga cewa [kisa] zunubi ne da rashin mutuntawa, haka kuma dukkan addinai sun haramta yin hakan.
“Haka kuma, cin mutunci ne ga al’ummarmu kashe jami’an tsaronmu da suke gudanar da aikinmu na hukuma. Sun naɗi bidiyon abubuwan da suka aikata tare da yaɗa su.
“An kashe su kuma an yanka gawarwakinsu. Mun fara kama waɗanda suka kashe jami’anmu. Waɗanda ke tsare a hannu suna taimaka mana da bayanai. Har yanzu muna aiki.
“Kun san ba za mu azabtar da wanda bai da laifi ba. Wannan zamanin ya wuce. Abin da ake kira tambayoyi kawai muke yi.
“Yana iya ɗaukarmu lokaci don samun bayanai daga gare su. Za mu sami da yawa kamar yadda zai yi wu daga wurinsu.
“Batun Neja-Delta yana da yawa. Wannan ya haɗa da yawan jama’a, tattalin arziki, kasuwancin mai da dai sauransu.”