Za mu zauna da Gwamnatin Oyo  kan dokar hana kiwo – Shugabannin Fulani

Al’ummar Fulani sun ce, ba za su yi jayayya da Gwamnatin Jihar Oyo kan sabuwar dokar hana kiwo da ta kafa a jihar ba. Kuma sun ce duk wanda ya ce zai yi fada ko kai karar gwamnati kotu a kan wannan lamari to yana rudar kansa ne. Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Alhaji […]

Za mu zauna da Gwamnatin Oyo  kan dokar hana kiwo – Shugabannin Fulani

Al’ummar Fulani sun ce, ba za su yi jayayya da Gwamnatin Jihar Oyo kan sabuwar dokar hana kiwo da ta kafa a jihar ba. Kuma sun ce duk wanda ya ce zai yi fada ko kai karar gwamnati kotu a kan wannan lamari to yana rudar kansa ne.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa ne ya fadi haka bayan taron Sarakunan Fulani da Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa da na jihohi a Legas, jim kadan da kammala bikin murnar cika shekara 25 da Sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammadu Bambado ya yi bisa karaga. Alhaji Muhammadu Kiruwa ya ce maimakon haka, shugabannin Fulanin za su zauna ne bisa teburi da mahukuntan jihar domin lalubo hanyar warware matsalar. “Sai in tura ta kai bango ne za mu yi zanga-zangar lumana tare da dakatar da fataucin dabbobi daga Arewa zuwa Kudu domin kwato hakkinmu,” inji shi.

Alhaji Muhammadu Kiruwa ya ce, “A matsayinmu na talakawa ba za mu iya hana gwamnati kafa doka ba, amma wannan dokar hana kiwo da kebe Fulani waje daya akwai gyara a ciki. Hakan ne ya sa taronmu ya amince da damka wa Sarkin Fulanin Legas alhakin tuntubar Gwamnatin Jihar Oyo domin zama bisa teburi daya da tattaunawa a samo mafita.”

“Wadansu daga cikin muhimman abubuwan da muke bukatar mika wa ga mahukuntan Jihar Oyo sun hada da amincewarmu da kafa dokar da suka yi amma su yi gyara da za ta hana kananan yara kiwon dabbobi da hana kiwo cikin dare da daure dukkan makiyayin da dabbobinsa suka lalata amfanin gona tare da biyan diyya ga manoma da daure dukkan Bayarben da ya kashe shanun makiyaya bayan ya biya diyya da hukunta dukkan makiyayin da aka kama da laifin satar mutane da garkuwa da su. Idan aka yi haka to za a zauna lafiya. Saboda haka nake kira ga shugabannin Fulani na kasa su bayar da hadin kai da goyon baya ga Sarkin Fulanin Legas domin ya samu saukin isar da wannan sako ga gwamnatin Oyo don cimma nasarar warware matsalolin da mutanenmu ke fuskanta a wannan sashe,” inji shi.

Sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammadu Bambado, wanda ya nuna amincewa da nauyin da shugabannin Fulani suka dora masa ya ce, za su yi fafutikar neman ’yancinsu har zuwa inda karfinsu zai kare. “Domin ba za mu yarda da irin wannan doka ta takurawa ga sana’o’inmu da muke bayar da gudunmawa ga bunkasa ayyukan gona da tattalin arzikin kasa ba. Babu fada babu zagi amma akwai hanyoyi masu yawa da za mu bi don kwato ’yancinmu cikin ruwan sanyi,” inji shi.