Za ta biya diyyar Naira miliyan 18 kan tsiyaye idon yaro
A ranar Litinin da ta gabata ne Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Nomansland a birnin Kano ta yanke hukuncin biyar diyyar Naira miliyan 18 da dubu 404 da 165 ga Murjanatu Sani da aka samu da laifin tsiyaye idon wani yaro mai suna Idris Abubakar mai shekara 12 a watan Disambar shekarar 2012.Alkalin kotun, Mai […]

A ranar Litinin da ta gabata ne Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Nomansland a birnin Kano ta yanke hukuncin biyar diyyar Naira miliyan 18 da dubu 404 da 165 ga Murjanatu Sani da aka samu da laifin tsiyaye idon wani yaro mai suna Idris Abubakar mai shekara 12 a watan Disambar shekarar 2012.
Alkalin kotun, Mai shari’a Faruk Ahmed ya ce tsiyaye idon Idris da Murjanatu ta yi laifi ne da ya saba wa sashi na 163 na dokar Final Kod ta shekarar 2000, don haka ne kotun ta yanke mata hukuncin biyan wannan diyya.
Alkalin ya ajiye ranar 24 ga Fabrairun nan don Murjanatu ta zo da kudin diyyar da aka nema daga wurinta.
Lauyan masu kara Barista danladi Musa ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya yi daidai, idan aka yi la’akari da girman laifin da matar ta aikata na lahanta idon yaron. “Za mu bi kadin wannan hukunci har sai matar ta biya diyyar, domin a tallafa wa rayuwar yaron da ta yi sanadin lahanta masa ido. An ba ta mako biyu ta je ta sayar da duk kadarar da ta mallaka ta kawo wa kotu kudin. Wannan kudi su ne za su taimaka wa yaron wajen daukar dawainiyar rayuwarsa da ta hada da lafiyarsa da kuma karatunsa. Idan muka yi sakaci a kan wannan diyya har yaron nan ya girma ba zai ji dadin abin da muka yi masa ba,” inji shi.
A nasa bangaren mahaifin yaron Malam Abubakar Attahiru ya nuna farin cikinsa da hukuncin da babbar kotun ta yanke.
Idan za a iya tunawa a bara Aminiya ta kawo labarin yadda wata kotun shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a karkashin Alkali Habibudden Sulaiman Sharifai ta yanke wa Murjanatu Sani hukuncin daurin wata daya a gidan kaso ko biyan tarar Naira 1,500 kan laifin sanadin tsiyayar da idon Idris Abubakar tare da ba da damar sulhuntawa a tsakaninta da iyayen yaron kan kudin diyya.
Sai dai kuma rashin gamsuwa da hukuncin da kuma rashin daidaitawa a tsakanin bangarorin biyun ne ya sa suka garzaya babbar kotun wadda ta yanke wannan hukunci.