Matatar Man Fatakwal Za Ta Fara Aiki Nan Da Makonni Biyu — Mele Kyari 

Mun yi alkawarin kammala matatar Kaduna a watan Disamba.

Matatar Man Fatakwal Za Ta Fara Aiki Nan Da Makonni Biyu — Mele Kyari 

Matatar Dangote ana tsaka da aiki

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Mele Kyari, ya ce nan da makonni biyu matatar man fetur da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas za ta fara aiki.

Kyari ya yi wannan bayani ne a gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Dattawa da ke sa ido kan ayyukan da ake yi na farfaɗo da matatun man fetur mallakin Najeriya.

Ya ce, kawo yanzu an riga an kai sama da gangar ɗanyen man fetur 450,000 matatar ta Fatakwal.

A tattaunawarsa da manema labarai bayan ya yi wa Sanatoci ƙarin haske, Kyari ya ce an kammala aikin injinan matatar Fatakwal da Warri, da kuma ta Kaduna.

Ya bayyana cewa matatar mai ta Kaduna za ta fara aiki a watan Disamba na wannan shekara.

Haka zalika ya ce, “Ina tabbatar muku wannan matatar ta Fatakwal za ta fara aiki nan da mako biyu masu zuwa.”

Da ya ke magana akan matatar man da ke Warri, ya ce “Ana can ana gwaje-gwajen da suka kamata a matatar man fetur da ke Warri, kuma nan ba da jimawa ba za a kammala.

“Matatar Kaduna za ta fara aiki a watan Disamba, ba mu kai matakin da muka kai a Warri da Fatakwal ba a Kaduna, amma mun yi alkawarin kammala matatar Kaduna a watan Disamba.”

Manajan Kamfanin na NNPCL ya tabbatar da cewa bututun da ke dakon ɗanyen man zuwa Fatakwal da Warri suna aiki, kawo yanzu kuma har sun kai sama da ganga 450,000 a matatar man ta Fatakwal.

Kyari ya ce za a iya samun matsalar tsaro, amma gwamnati tana nan, kuma ya san za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da aikin ya yi nasara.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin, Sanata Ifeanyi Ubah, ya ce mataki na gaba shi ne kwamitin ya ziyarci matatun man domin ganewa idanun sa irin aikin da ake yi.