Za ta mayar wa mijinta sadaki don ya sake ta
Wata matar aure mai suna Khadija Salisu ta yi karar mijinta a Kotun Musulunci da ke Magajin Gari, Kaduna, inda ta bukaci ta mayar masa da sadakinsa Naira dubu hamsin domin ya sake ta. A cewarta, ba ta sha’awar ci gaba da zama da shi a matsayin matarsa, sakamakon kasancewarsa a daure a gidan yari. […]

Wata matar aure mai suna Khadija Salisu ta yi karar mijinta a Kotun Musulunci da ke Magajin Gari, Kaduna, inda ta bukaci ta mayar masa da sadakinsa Naira dubu hamsin domin ya sake ta.
A cewarta, ba ta sha’awar ci gaba da zama da shi a matsayin matarsa, sakamakon kasancewarsa a daure a gidan yari.
“Na yi kararsa ce saboda ina son in mayar masa da sadakinsa domin ya sake ni. Ba na bukatar ci gaba da zama da shi,” inji ta.
Matar ta ce shekararsu daya da wata shida da aurensu kafin a tsare shi a gidan yari.
Alkalin Kotun, dahiru Lawal ya tambaye mijinta Adamu Abdullahi ko ya ji abin da matarsa ta ce, na neman mayar masa da sadakinsa?
Sai ya ce “Na ji abin da ta ce amma fa ni ina son matata.” Ya tabbatar wa kotun cewa ana tsare shi ne a gidan yarin Kaduna a bisa zargin yin fyade, wanda ya ce ya kwashe wata shida a tsare.
Da alkalin ya tambaye shi ko nawa ya biya a matsayin sadakin matarsa, sai ya ce Naira dubu hamsin. Don haka sai alkalin ya umurci matar ta biya shi sadakinsa, inda ita kuma dauki alkawarin biyansa kudin nasa a mako mai zuwa.
Alkalin ya bayyana wa wanda ake karar cewa Musulunci ya bai wa mata damar neman saki daga mazansu ta hanyar khul’i idan ba su bukatar ci gaba da zama da su.
“Saboda haka, ni dahiru Lawal, Alkalin Kotun Shari’a da ke Magajin Gari; na tabbatar da rabuwar aure a tsakanin Khadija da Adamu, za ta kuma mai da masa sadakinsa,” inji shi.