Za ta tura ’yan sandan Najeriya koyon dinki a Pakistan
Rundunar ’yan sandan Najeriya za ta tura wasu jami’anta zuwa kasar Pakistan domin koyon yadda ake dinka yunifom din ’yan sanda.Mataimakin Kakakin Rundunar ta kasa Abayomi Shogunle ne ya shaida wa jaridar Premium Times haka a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce idan jami’an suka dawo, ana sa ran su rika dinka wa […]
Rundunar ’yan sandan Najeriya za ta tura wasu jami’anta zuwa kasar Pakistan domin koyon yadda ake dinka yunifom din ’yan sanda.
Mataimakin Kakakin Rundunar ta kasa Abayomi Shogunle ne ya shaida wa jaridar Premium Times haka a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce idan jami’an suka dawo, ana sa ran su rika dinka wa ’yan sandan yunifom.
“A wani bangare na inganta yunifom din ’yan sanda, za mu aika wasu jami’anmu na ’yan sanda zuwa kasar Pakistan domin su koyo yadda ake dinka yunifom domin su dinka wanda ya dace da na kasashen duniya,” inji Shogunle.
Ya ce tunanin tura jami’an koyon dinki a Pakistan ya zo ne bayan da Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya ya lura da bukatar a yi waje da bakin yunifom din ’yan sanda zuwa mafi kyau mai ruwan bula.
Shogunle ya ce rundunar ta zabi Pakistan ne saboda ficen da ta yi a nau’o’in dinki na jami’an tsaro. Ya ce kasar tana kuma daga cikin kasashen da ke sahun gaba wajen sana’anta yunifom din jami’an tsaro da yadudduka da sauran kayan masaku.
Ya ce za a ba da cikakken yunifom kyauta ga kurata zuwa sufetoci, yayin da manyan jami’ai daga mukamin mataimakin sufurtanda (ASP) zuwa sama za su dan biya wani.
Duk da Mista Shogunle bai bayyana nawa manyan jami’an ’yan sandan za su biya ba, ya ce za a rika karbar yunifom din ne daga shagunan jami’an ’yan sandan Najeriya. Ya ce ba za a bayyana farashin yunifom din ba, ko kuma guda nawa kowane mutum zai amsa, saboda dalilai na tsaro.
Ya ce ba a ajiye rana ta daina amfani da bakin yunifom din ’yan sandan kwata-kwata ba, “Sai dai muna ci gaba ne da gwajin wasu samfurori, amma abin da zan iya fadi shi ne lokacin da aka gabatar da sabon yunifom din, zai kasance irin wanda ake ganin ’yan sanda da shi a kasashen da suka ci gaba”.
Ya ce an tura samfuri yunifom din da ake bukata ga wasu masana’antu a kasar Pakistan, inda idan aka dawo da samfurin kuma aka kammala gyare-gyare, in akwai, rundunar ’yan sandan Najeriya za ta fara yin sabon yunifom din, da zarar ’yan sandan da suka dawo daga koyon dinki daga Pakistan kuma aka samar da kayayyakin aiki.