Za ta yi tafiyar mil 30 don ta ki biyan kudin tasi
Wani alkali a wata kotu da ke Jihar Ohio ta kasar Amurka ya umarci wata mata da ta yi tafiyar mil 30 (kimanin kilomita 48) da kafarta saboda ta ki biyan wani dan tasi da ya yi tafiyar mil 30 da ita motarsa kudinsa. An dai kama matar ce mai suna, bictoria Boscom da wani […]
Wani alkali a wata kotu da ke Jihar Ohio ta kasar Amurka ya umarci wata mata da ta yi tafiyar mil 30 (kimanin kilomita 48) da kafarta saboda ta ki biyan wani dan tasi da ya yi tafiyar mil 30 da ita motarsa kudinsa.
An dai kama matar ce mai suna, bictoria Boscom da wani saurayinta bayan sun tsere ne daga wata tasi ba tare da biyan direban ba, wanda ya yi tafiyar mil 30 da su, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News blog ta bayyana.
Alkalin mai suna Cicconetti ya bai wa bictoria zabi biyu: kodai ta yi zaman gidan yari na kwana 60 ko kuma ta yi tafiyar mil 30 da kafarta a cikin kwana biyu (kimanin fiye da nisan Kaduna zuwa garin Jaji). Amma sai ta zabi ta yi tafiyar. Kodayake, alkalin ya ce za ta yi hakan ne tare da wata na’urar da zata dinga bayyana bayanan wura-wuren da take.
Har ila yau, an umarce bictoria da ta biya dan tasin dala 100 (kimanin naira dubu 20)da kuma gudanar da aikin karfi na tsawon kwanaki uku.