Zababben Shugaban Ghana mutum ne mai saukin kai da daraja mutane – Isyaku Ibrahim

Alhaji Isyaku Ibrahim dattijo ne mai shekara 78, wanda tun yana dan shekara 21 ya fara siyasar neman mulkin kai. dan siyasar kuma dan kasuwa ya tattauna da Aminiya game da hali abokinsa sabon zababben Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo kuma ya ja kunne ga shugabannin Afirka game da rikicin kasar Gambiya. Mene ne tarihin […]

Zababben Shugaban Ghana mutum ne mai saukin kai da daraja mutane – Isyaku Ibrahim

Alhaji Isyaku Ibrahim dattijo ne mai shekara 78, wanda tun yana dan shekara 21 ya fara siyasar neman mulkin kai. dan siyasar kuma dan kasuwa ya tattauna da Aminiya game da hali abokinsa sabon zababben Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo kuma ya ja kunne ga shugabannin Afirka game da rikicin kasar Gambiya.

Mene ne tarihin abokinka Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo?
Na san shi da mahifinsa fiye da shekara 40 da suka wuce. Mutum ne mai saukin kai da daraja mutane da tsantseni. A takaice, ya zama tilas mutanen Ghana su yi ta yin murna domin sun mori Shugaban kasa da zai fitar da kasar daga kunci da yardar Allah. Yana da dukiya matuka, kuma yana da ilimi da wayewa na sanin duniya.

Yaya aka yi talakawa ba sa shan wahalar ganinsa, wato koyauhse kofarsa a bude?
Lallai mahifinsa mutum ne mai jama’a da son jama’a. Mahaifinsa tare suka yi karatu da matar tsohon Cif Jojin Najeriya Uwargida Adetokunbo Ademola. Sun yi karatu a Jami’ar Ingila. Mahaifinsa yana da hangen nesa, don ya gina babban gida sannan ya koma Unguwar Madina ta kasar Ghana inda Hausawa suka fi yawa har ya fara saye da sayar da shanu. Nana Akufo-Addo ya tashi cikin talakawa kuma baya kyamar jama’a ko kadan. Wannan ya kara sanyawa ya karbu a wurin jama’a, saboda ba ya kyamar jama’a.

Me ya sa tsarin kamfen dinsa ya yi zarra a karo na uku bayan ya fadi zabe har sau biyu a baya?
Ya kwaikwayi halin mahaifinsa ne na son jama’a da sanin gaskiya da daraja mutane da kuma kyamar yin facaka, shi mutum ne da ba ya cin bashi don ya burge kowa. A takaice, akwai lokacin da ke sayen tsire da yawa, sai na ce masa, shin bashi kake karba don ka burge ni? Sai ya ce ai in har mahaifinsa ya ji yana karbar bashi, zai sha wahala da bakin gwale-gwale. Domin an koya masa cewa ba a cin bashi don burgewa saboda an ce, son zuciya bacin zuciya, (dariya). Game da tambayarka, ai yanzu kan mage ya waye, gaskiya ta fito fili. kila a baya an yi irin abin nan ne na masu mulki a Afirka.

Me ya sa mahaifinsa ya zama Shugaban kasa maraiko daga daga 1970 zuwa 1972?
Mahaifinsa lauya ne kamar shi sabon Shugaban kasa mai jiran gado. Bayan ya zama Alkalin Alkalai sai aka nada shi Shugaban kasa mara cikakken iko. Sojoji ne suka kirkiro ofishin na Shugaba mara cikakken iko. Su kuma soja su suke da mukamin Shugaban Gwamnati mai cikakken iko. Kuma mahaifinsa yana daya daga cikin wadanda suka yi yakin karbo wa kasar mulkin kai.

Me ya sa kuka bar kasar Ingila kuka koma Faransa?
Mun je kasar Faransa ne daga kasar Ingila domin koyon Faransanci, amma mun je ne a lokaci mabambanta. Amma fa ni na yi gaba, shi ya tsaya shi ya sa ya fi ni jin Faransanci. Yana jin Faransanci fiye da Ingilishi. Duk yadda muke ban taba yi masa Hausa ba, amma na san yana jin harshen tunda a cikin Hausawa ya tashi. Duk da na je na yi masa murna a farkon wannan makon, amma ban yi masa Hausa ba. Amma duk ran da muka sake haduwa zan jaraba shi (dariya).

Me yasa shi da mahaifinsa suka bar kasar Ghana don yi gudun hijira a Najeriya?
Juyin mulkin da soja karkashin Sojan Sama Jerry Rawlings suka yi ne ya sa suka gudu suka yi hijira. Lokacin da suka yi wa Shugaban kasa Hila Lima juyin mulki. Da suka iso Najeriya lokacin mulkin Shugaba Shehu Shagari, sai ya hada su da Alhaji Umaru Shinkafi don ya ba su masauki a birnin Legas.

Yaya aka yi kai da abokinka kuka bude kamfani a kasar Faransa?
Ni dan siyasa ne. Kuma matata ’yar kasar Liberiya ce. Da muka je hutun karshen shekara a kasar, sai muka ji a rediyo cewa an yi juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Sai Jakadan kasar Amurka a Liberiya wanda kuma makwabcina ne ya same ni da safe ya ce, “Wa nake tsammani zai zama Shugaban kasa?” Sai na ce, “Ko Muhammadu Buhari ko Ibrahim Babangida, domin a lokacin ba a dade da kara musu girma daga mukaman Birgediya zuwa Manjo Janar ba. Sai ko Manjo Janar Muhamamdu Buhari ya zama Shugaban kasa. Daga nan ni da abokina, Nana Akufo-Addo da Aled Martin Mills muka nufi Landan sannan muka zarce Faransa inda muka bude kamfani. Da yake shi Nana Akufo-Addo lauya ne da yake aiki a Paris, shi ya sa ba mu sha wuya ba wajen bude kamfanin. Ni ne shugaban kamfanin, shi kuma mataimakina.

Shin ko yana da burin siyasa a lokacin?
kwarai kuwa, yana da burin siyasa domin yana da burin ba da gudunmawa don tallafa wa kasa baki daya kamar yadda iyayensa suka yi.

Don me Shugaban kasar Ghana da aka kayar a zaben 7 ga Disamba, Mista John Mahama ya ce lallai Nana Akufo-Addo gwarzo ne?
Ba shi da girman kai, kowa na iya zuwa ya gan shi, ba ya yaudara. Haka ya hori manyan da ke kusa da shi su yi.

Wace shawara za ka ba shi don ya cimma cika burin kamfen din da ya yi wa jama’a?
Lallai na hakikance cewa mutum ne shi da ba ya cin hanci da rashawako handama da babakere, yana da son jama’a, yana son talakawa suna sonsa. Don haka ina fata ya ci gaba da halayensa don a gudu-tare-a-tsira-tare.Ya kula da abin da talakawa ke so ya yi musu da samar da tsaro da tattalin arziki da lumana.

Ghana tana da fetur, amma farashinsa ya fadi a kasuwar duniya, ta yaya kake ganin zai samu kudin da zai cika alkawuran siyasa ta hanyar yi wa jama’a aiki?
Mene ne sunan kasar kafin a sauya shi zuwa Ghana? Gold Goast, wato kasa mai albarkacin zinari. To har yanzu suna da zinari a kasar. Kuma ba su dogara kan fetur kacokan ba, kamar yadda muka yi a Najeriya. Su manoma ne don suna da gahawa da sauransu. Kuma sun fi ’yan Najeriya bin doka da oda.

Ko za ka yi karin bayani?
Suna da tsantseni kwarai da gaske, sun waye, suna da son kasa ba irinmu ba ’yan bangaranci kamar yadda ta yi kullum.

Kana ganin mataimakinsa, masanin harkar kudi kuma mataimakin Shugaban Babban Bankin Ghana abokin tafiya ne?
kwarai kuwa, don yana da ilimi, kuma lallai za su hada kai su ba marada kunya.

Wata sabuwa a siyasar Afirka ita ce yadda Shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh ya yi amai ya lashe, inda ya amsa ya shan kaye daga baya ya ce, sai dai a sake sabon zabe. Me kake gani hakan zai janyo?
Lallai na tallafa wa abokaina sun ci zabe a wurare da dama kamar tsohon Shugaban kasar Amurka Mista Bill Clinton da sauransu. To lallai wannan kalubale ne ga shugabannin kasashen Afirka. Domin bai kamata su bar wani daga cikinsu ya yi wa dimokuradiyya karan-tsaye ba. Ya mika mulki kawai. Ya kamata su yi hangen nesa, domin mutanen Afirka ne kadai za su iya gina Afirka ba wadansu daga wajenta ba. Lokaci ya yi da za su tabbatar an bi doka a Gambiya. Su kuma daina mulkin danniya, su yi mulkin kwarai don kan mage ya waye.

Wace shawara za ka ba bangaren Zartarwa da na Majalisa da na Shari’a don gina Najeriya?
A’a, a’a, a’a. Ba zan ce komai ba game da salon siyarsar Najeriya a yanzu. Ina matashi na yi siyasar karba wa Najeriya mulkin kai. Aminu Kano da Azikiwe da Tafawa dalewa da Sardauna da Awolowo duk iyayen gidana ne. Na tallafa an kafa gwamnatoci a Najeriya ta siyasa a karo daban-daban, ni dai burina shi ne a gina kasa.