Zababbun Tatsuniyoyi 19 Cikin Ajami: Yunkurin inganta tarbiyyar mata da farfado da Ajami

Sunan Littafi: Taskar Tatsuniyoyi: Zababbun Tatsuniyoyi 19 Marubuci: Bukar Usman Marubucin Ajami: Rufa’i Sani Shekarar Wallafa: 2017 Kamfanin Wallafa: Mate ni kani, Albasa (Nijar) da Gidan Dabino Publishers, Kano-Najeriya Yawan Shafuka: 240 Farashi: Ba a fada ba. Rubutu cikin harshen Hausa ta amfani da haruffan Larabci (Ajami) domin isar da sako ko adana tarihi da […]

Zababbun Tatsuniyoyi 19 Cikin Ajami: Yunkurin inganta tarbiyyar mata da farfado da Ajami

Sunan Littafi: Taskar Tatsuniyoyi: Zababbun Tatsuniyoyi 19

Marubuci: Bukar Usman

Marubucin Ajami: Rufa’i Sani

Shekarar Wallafa: 2017

Kamfanin Wallafa: Mate ni kani, Albasa (Nijar) da Gidan Dabino

Publishers, Kano-Najeriya

Yawan Shafuka: 240

Farashi: Ba a fada ba.

Rubutu cikin harshen Hausa ta amfani da haruffan Larabci (Ajami) domin isar da sako ko adana tarihi da sauran bukatu irinsa ya dade a kasar Hausa, musamman tun kafin zuwan Turawa kasar Hausa. Wannan kuwa bai zo da mamaki ba, musamman ganin yadda tarihi ya tabbatar da cewa kasar Hausa ta fara yin musharaka da Larabawa kafin zuwan Turawa. Duk da cewa a halin yanzu Hausar Boko ta kwace Hausar Ajami, har yanzu rubutun Ajami na da tasiri, musaman a lunguna da karkarar kasashen Hausa, musamman a kasashen Najeriya da Nijar da wasu da dama a kasashen Afrika ta Yamma. Domin isar da sako na kai tsaye ga daliban makarantun tsangaya a kasar Hausa, shi ya sanya wata kungiya mai zaman kanta mai suna IRENE SAHEL ta ga dacewar amfani da Ajami wajen isar da muhimman sakonnin inganta rayuwar ’ya’ya mata. Dalili ke nan kuma suka zabi muhimman tatsuniyoyi 19 daga babbar Taskar Tatsuniyoyi da shahararren Marubuci, Dokta Bukar Usman ya tattara.

Tun da farko, an zabi tatsuniyoyi guda goma sha tara ne daga littattafai goma sha hudu na Taskar Tatsuniyoyi. Dukkan tatsuniyoyin guda 19 suna dauke da muhimmin jigo ne da ke da alaka da mata. Jigogin da suka danganci tarbiyya, sana’a, zaman aure da sauran harkokin rayuwa da suka jibanci mata.

 Daga dukkan alamu, an yi la’akari da ma’anar tatsuniya wajen zaben kunshiyar wannan littafi na Ajami. “Tatsuniya labari ne dauke da wasu halaye nagari da hanyoyin warware wasu matsaloli na rayuwa da kuma yin ishara game da wasu abubuwa da sukan faru ga masu aikata munanan halaye, kamar mugunta da kwadayi da wulakanci ko zalunci ko kishi ko sata da cuta da sakarci da karya; ko kuma ga masu aikata kyawawan halaye, kamar aikata alheri da nuna mutunci da soyayya da ladabi da biyayya da rikon amana da sada zumunci da nuna tausayi da girmama na gaba da sauransu.” (Taskar Tatsuniyoyi).

Tatsuniya ta farko, mai taken ‘Marainiya’ tana ba da labarin wata yarinya ce da ta taso a matsayin marainiya, wacce ba ta da uwa kuma ba ta da uba. Ta fuskanci matsaloli da yawa a rayuwarta, inda daga karshe ta taki sa’a ta kai ga auren yarima, dan sarki.

Darussa hudu wannan tatsuniya ke koyarwa ga yara, musamman ma mata. Tana koya darasin cewa rabon kwado ba ya hawa sama. Idan abu rabonka ne, komai yadda aka so kange ka daga gare shi sai ka samu. Darasi na biyu shi ne, mai nema yana tare da samu. Gaskiyar haka ta fito daga ayyukan Marainiya, wacce ta tarbi hadari, ta tafi nemo kashin wata tsutsa mai cin mutum, inda ta kwashe shekara biyu tana tafiya, sannan ta isa garin. Ta samo kashin tsutsar, wanda da shi ne ta samu nasarar warkar da yarima dan sarki da ya dade babu lafiya kuma duk bokayen gari sun gaza warkar da shi. Darasi na uku shi ne, mai rabon ganin badi, ko ana ha maza ha mata sai ya gani, kamar dai yadda Marainiya ta fuskanci hadurra da dama a rayuwa, amma ta kubuta. Sai kuma darasi na hudu da ke nuna cewa hassada ga mai rabo taki ce. Marainiya ta sha kaidin gaba da hassada daga kishiyar innarta, amma daga karshe ita ta samu nasara a rayuwa.

Tatsuniya ta biyu a littafin, ita ce: ‘Wani Sarki Da Matansa.’ Muhimman darussa biyu ke cikin wannan tatsuniya, wacce ke nuna ishara ga mata da cewa su guji mugunta ga kishiya. Tana nuna cewa mugun nufi ba ya kashe dan kurciya. Haka kuma darasin kaikayi koma kan mashekiya ya fito a cikinta, musamman yadda kishiyoyi biyu suka samu hukuncin kisa saboda hada kai da suka yi suka cutar da jaririya, diyar amaryar saki, saboda bakin ciki da bakin kishin cewa su ba su taba haihuwa ba.

Tatsuniya ta uku da ke kunshe cikin wannan littafi na Ajami ta kasance mai taken ‘Mace Mai Ciki.’ Manyan darussan da take koyarwa sun hada da muhimmancin cika alkawari. Idan ka dauki alkawari, ka yi kokari iyawarka ka cika, domin kamar yadda Hausawa suka ce, alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta. Tana nusar da cewa sa’a kan zo wa mutum a rayuwa, inda mutum kan iya tsintar dami a kala. Haka kuma akwai darasin da ke bayyana cewa rabon kwado ba ya hawa sama.

A tatsuniya ta hudu, mai taken ’Yan Mata Masu Kamun Kifi’ an koyar da darussa guda uku kwarara, muhimmancin alheri da sakamakon da yake haifarwa, amfanin rufin asari da yadda Allah ke taimakon bawanSa, sai kuma munin karya da yadda komai daren dadewa asirin mai karya kan bayyana.

Sai kuma tatsuniya ta biyar mai taken, ‘Jarumin Sarki’ wacce take koyar da darussan da suka hada da illar da ke tattare da karya alkawari da illar cin amana. Haka kuma tana bayyana muhimmancin kauna da soyayya a matsayin amanar ruhin zuciya.

‘Kishiyoyi Biyu’ ita ce tatsuniya ta shida a jerin kunshiyar tatsuniyin da ke cikin littafin nan na Ajami kuma tana koyar da muhimman darussa guda hudu ne, wadanda suka hada da illar munafunci da yadda munafuki ke karewa, domin kuwa an ce munafunci dodo ne, yakan ci mai shi. Tana nuna tasirin kaddara, cewa duk abin da ka ga ya faru da mutum, to an kaddara masa faruwarsa tun farkon halitta, kuma ba zai iya kauce masa ba. Tana koya illar hassada, kamar kuma yadda take nuna muhimmancin hakuri da yadda mutum mai hakuri ke samun albarka da alheri a rayuwa.

Darussa abin lura guda uku ne suka bayyana a tatsuniya ta bakwai, mai taken ‘Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu.’ Tana nuna muhimmancin yin biyayya da yadda mai biyayya ke cin ribar lamurransa na rayuwa. Tana bayyana yadda kowane mutum ke da irin tasa baiwa da ta bambanta da ta wani. Haka kuma tana nuna cewa duk abin da ka iya, akwai wanda ya fi ka, ko mugunta ko alheri.

‘Yarima Da Labi’ ita ce tatsuniya ta takwas a wannan littafi, wacce kuma take ishara da cewa alheri dai abin so ne kuma yana da amfani a rayuwa domin idan ka aikata shi, wata rana sai ka tsinci abinka ko kai tsaye ko kuma ta wata hanyar daban. Haka kuma tana nuna cewa matar mutum kabarinsa, wani ba ya auren matar wani a rayuwa, kamar dai yadda ta kasance tsakanin Yarima da Labi.

Tatsuniyar ’Yar Sarkin Da Ta Saci dinya’ ita ce ta kasance lamba ta tara a littafin kuma tana nuna muhimmancin hukunta mai laifi komai matsayinsa a cikin al’umma. Haka kuma tatsuniyar na ishara da cewa kowace al’umma tana da ka’idojinta da dokokinta na al’ada, wanda binsu shi ne zaman lafiyar al’umma.

Tatsuniya ta goma, ita ce mai taken ‘Tsurondi.’ Tsurondi dai wani dodo ne da ke rikida zuwa mutum. Tatsuniyar dai tana koyar da muhimmancin alkawari kuma tana nuna yadda Allah kan taimaki bawanSa ta inda ma bawan bai sani ba kuma bai zata ba. Tana nuna mhummancin hankali da tasirin mutum mai hankali wanda komai karancin shekarunsa ya dara babban da ya kasance wawa. Tana kuma koya darasin cewa ga duk wanda bai jin bari, to ba zai rasa gani ba. Kamar ta masu iya magana da suka ce, mai rabon shan duka, ba ya jin kwaba sai ya sha.

Sauran tatsuniyoyi tara da littafin nan na Ajami ke dauke da su sun hada da ‘Binta ’Yar Sarki’ da ‘Wata Mayya Da danta’ da ’Yan Bakwai Da Aljana’ da ‘Makauniya Da danta’ da ’Yar Mowa Da ’Yar Bora’ da ‘Wata Mata Da Aljani.’ Sauran sun hada da ‘Nasiru Da Nisiru’ da ’Yan Mata Biyu’ da kuma tasuniya ta goma sha tara kuma ta karshe, watau ‘Darajar Neman Aure.’

Babu shakka wannan littafi yana dauke da darussa masu muhimmanci ga rayuwar al’umma, musamman ma yadda aka zabo su kacokan don su dace da koyar da mata. A ta’alikinsa ga littafin Taskar Tatsuniyoyi, Shaihun Malamai, Farfesa Bello Sa’idu na Jami’ar Bayero Kano yana cewa: “Malamai sun dade da nuna muhimmancin tatsuniya a rayuwar Bahaushe; sun yi rubuce-rubuce da dama a kanta. An sani kuma cewa asalin tatsuniya kirkiro ta ake yi, kuma da ake yada ta, amma saboda fa’idojin da ta tattara aka ga wajabcin tattara ta a wallafa a littattafai domin amfanin masu tasowa, musamman saboda hangowar zamani ya fara gurbata tunanin yara da bakin al’adu masu janye hankalinsu da shagaltar da su duk wata al’ada da suka gada iyaye da kakanni.” (Shafi na ddi).

Wannan littafi na Ajami, an inganta shi da kyakkyawan bango mai dauke da kyakkyawan hoto mai daukar hankali. Haka kuma a shafukan cikinsa ma, an kayata shi da zanen hotuna da ke ishara da wasu tatsuniyoyin, wanda haka kan kara jan hankali ga musamman yara su kara maida hankali wajen fahimtar darussan tatsuniyoyin.

Littafin nan zai taimaka wajen isar da sakonni masu girma da muhimmanci ga yara, musamman ma masu karatun tsangaya kuma zai taimaka wajen dawo da martabar rubutun Ajami a cikin al’umma.

Wani abu da na tsinkaya a yayin nazarin wannan littafi shi ne, an yi amfani da Hausar Mutanen Nijar wajen rubuta wasu kalmomi, maimakon a yi amfani da Amsasshiyar Hausa. Misali wajen rubuta “Gata-Gata” sai aka rika rubuta “Kata-Kata.” Haka kuma maimakon a rika rubuta “Tatsuniyoyi” sai aka rika rubuta “Tasuniyoyi.” Kuma ba a yi amfani da haruffa masu kauri ba sosai, wasullan ma ba su fito ba sosai yadda ya dace, wanda hakan zai wahalar da mai karatu, musamman ma a Arewacin Najeriya. Don haka, yana da kyau idan an tashi sake wallafa littafin, a gyara wadannan kura-kurai, domin a samu damar cin ma burin ilimantarwa da fadakarwa yadda ya dace.