Zabaya ya rataye kansa don an tsangwame shi

Wani matashi zabiya mai kimanin shekaru 23 mai suna Ugochukwu Ekwe ya kasha kansa a ranar lahadin data gabata saboda launin fatarsa.An gano gawar matashin ne rataye a jikin fankar sama a gidan da ya ke zaune da iyalansa a unguwar Festac a jahar Legas. Bincike ya nuna cewa Ugechukwu kafin ya rataye kansa ya […]

Zabaya ya rataye kansa don an tsangwame shi
Zabaya ya rataye kansa don an tsangwame shi

Wani matashi zabiya mai kimanin shekaru 23 mai suna Ugochukwu Ekwe ya kasha kansa a ranar lahadin data gabata saboda launin fatarsa.
An gano gawar matashin ne rataye a jikin fankar sama a gidan da ya ke zaune da iyalansa a unguwar Festac a jahar Legas.
Bincike ya nuna cewa Ugechukwu kafin ya rataye kansa ya fara yajin cin abinci tun ranar Asabar a dalilinsa na cewar mutane na nuna masa wariya da tsangwama. Kuma yaki ya je majami’a tare da ‘yan uwansa  a ranar Lahadin data gabata. A lokacin da ‘yan uwan nasa suka dawo daga cocin ne suka gano gawarsa na lilo a jikin fankar sama nan take sukayi kururuwar ankarar da jama’a halin da ake ciki. An dai  hakikance cewa zabiyan ya dade yana kokarin kashe kansa tun a baya.
Wani makwabcin gidan da lamarin ya abku wanda da bai so a bayyana sunansa ba ya ce “a sa’ilin dana dawo daga majami’a sai naga anyi cirko-cirko a gaban gidan su, dana tambaya kome ya faru sai aka fadamin cewa Ugochukwu ne ya kashe kansa. Ya kammala karatunsa na sakandare tun shekarar 2009. An ce tuntuni yake yunkurin kashe kansa sabo da tsangwamar dayace ana nuna masa. Munga ‘yan sandan dake aiki a unguwar festac sunzo sun tafi da gawrar tasa, mahaifiyarsa tare da ‘yan uwansa nata rusa kuka”.
Kakakin ‘yan sandan Legas Patricia Amadi tace bata sami cikakken bayani ba daga comandan shiyar “E” Mista Frank Mba, sai dai tayi alkawarin karin bayani dazarar hakan ya samu.