Zabe ba yaki ba ne, hanya ce ta kawo canji cikin lumana

Ganin yadda zabubbuka ke karatowa da kuma ganin yadda ake ta tada jijiyar wuya tsakanin ’yan takara da magoya baya, MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta bijiro da fadakarwa da jan hankali ga al’umma, yadda za a kauce wa rikice-rikice kafin ko bayan zaben nan mai karatowa. Ga abin da take cewa: Sanin kowa ne […]

Zabe ba yaki ba ne, hanya ce ta kawo canji cikin lumana
Zabe ba yaki ba ne, hanya ce ta kawo canji cikin lumana

Ganin yadda zabubbuka ke karatowa da kuma ganin yadda ake ta tada jijiyar wuya tsakanin ’yan takara da magoya baya, MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta bijiro da fadakarwa da jan hankali ga al’umma, yadda za a kauce wa rikice-rikice kafin ko bayan zaben nan mai karatowa. Ga abin da take cewa:

Sanin kowa ne a kasar nan zaben 2015 saura ’yan kwanaki kalilan suka rage a aiwatar da shi. Amma me ke faruwa tsakanin ’yan kasa?
Abin da yake faruwa shi ne, tunani mabambanta. Kowane dan kasa da tunaninsa a kan wannan zaben. Kowa ya san yana da nasa tunanin, na abin da yake ganin zai yi ko zai faru a lokacin zaben. A cikin wadan nan tunane-tunen ne na ’yan kasa muke son mu dauki kwaya biyu, mu yi magana a kansu kamar haka:
Tunanin kawo canji ko tunanin ta zarce. Da yawa daga cikin ’yan kasar nan, ba abin da ke kai-kawo cikin zukatansu irin tunanin ta yaya za a yi su yi amfani da kuri’unsu, su canza wata jam’iyya zuwa ga wata ko canza wani mukamin siyasa zuwa ga wani ko tabbatar da ta zarcen wata jam’iya ko mukamin wani, domin samun canjin gudanarwar mulki ko kuma kauna ga tabbatuwar wani a kan mukamin da yake a kai.
Amma ya kamata ga dukkan mai tunanin kawo canji ko ta zarce ya fara tunanin hanyar da zai bi don samun tabbatuwar abin da yake fata, cikin hanyar zaman lafiya da lumana. Yana da kyau mu yi kokari iya kokarinmu, mu ga mun gina tunaninmu da tubalin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin a duniyar nan ba abin da ya kai zaman lafiya dadi da alfanu a zamantakewar rayuwa. Akwai hanyoyi da dama da za mu iya bin su mu ga mun yi zabenmu lami lafiya, ba tashin hankali ko fitina.
Muna iya shirya tarurruka a cikin unguwanninmu da garuruwanmu, domin mu tattauna hanyoyin samar da zabe cikin lumana. A cikin taron, muna iya samar da wata kwarya-kwaryar kungiya mai hadakar maza da mata da za ta yayata wa al’ummarmu alfanun zabe cikin lumana, tare da ture dukkan wasu matsaloli da ke kawo tarnaki a lokutan zabe. Aikinta zai ratsa gidaje, makarantu, kasuwanni, wuraren ibada, da dai dukkan wata mahadar jama’a, don tabbatar da samun sahihin zabe mai inganci cikin kwanciyar hankali.
Zai yi kyau sarakuna, limamai da dai sauran al’ummar kasar nan kowa ya rika tunanin irin gudunmawar da zai iya bayarwa don ganin an yi wannan zabe na bana cikin kwanciyar hankali da lumana. Gaskiya lokaci ya yi da za mu gaya wa kanmu gaskiya. Mu yi wa kanmu fada a kan wautar da mukan yi a lokutan kakar zabe. Mu tuna baya mu ga yadda muka sha wahala, muka rasa da yawan rayukan ’yan uwanmu, muka rasa muhallanmu, muka kaurace wa gidajenmu, muka aibanta junanmu, muka haddasa gaba da kiyayya a tsakaninmu, wai domin siyasa. Kuma abin haushi da ban takaici shi ne, duk wannan hasara da ta faru ta kare ne a kan talaka.
Talaka shi kadansa da iyalansa abun yake karewa a kansu. Mu dauki misali da zaben 2011, mu auna mu ga abin da ya faru. Shi ne an samu rashin sahihancin zabe a wasu wurare sai talakawa suka yi bore da tarzoma don nuna fushinsu, suka hau kashe-kashe da kone-kone a tsakaninsu da hukuma. Ana haka sai ya juya zuwa fadan kabilanci da na addini. Shekaru hudu ke nan da faruwar lamarin amma har yanzu da yawan wasu daga cikinsu suna sansanin ’yangudun hijira. Da masu neman canji da masu fafutukar ta zarce, ba wanda zai iya bugun kirji ya ce shi ya yi nasara, dukkansu sun yi tarayya a sansanin gudun hijira kuma gwamnati da su ’yan siyasar da ake yi wa yakin, kowa ya kawo ido ya sa musu, kusan ma mu ce an manta da su a can. To mene ne alfanun hakan? Babu, sai dai koma baya da lalacewa.
Mu sake daukar misali da masu yin bakar bangar siyasa. Wane alfanu ake samu a cikinta? Babu, bana shekara 15 ke nan ana satar kuri’u, ana zari-ka-ruga, ana sayar da katin zabe, ana sayar da ’yanci kan ’yan kudi kalilan, ana ka-ci-ba-ka-ci-ba-ka-ci, da dai duk wani nuku-nuku na sarari da na boye. Amma in ban da bakar azaba, ba abin da muka amfana da shi sai koma bayan siyasa da muke ta fuskanta. Duk kasashen da suka ci gaba sun tafi sun bar mu, domin su idan lokacin zabe ya zo musu, sukan dauke shi lokaci ne na annashuwa da jaraba ’yancinsu, don sake zabar shuwagabanni nakwarai.
Sabanin yadda yake kasancewa a nan kasar tamu, domin mu namu lokacin zaben yakan zama lokaci ne na fargaba da zullumi da taraddadi a gare mu, domin mun san ba mu da tabbas a kan zabinmu; ba mu da yakini a kan za mu zauna lafiya bayan zaben, ga cin karo da bakar wuya. Ita kanta jefa kuri’ar sai mun gaji, mun galabaita kafin mu samu mu yi ta. Ba wani cikakken tsari mai dadi, komai cikin wahala muke yinsa amma duk da haka sai ka tsinci talaka da sakarcin rashin gane hakan. Ya wahala lokacin zabe, ya wahala bayan zabe, in an kafa gwamnati ma shi ne a wahale, domin daga ranar da aka rantsar da zababbu amfanin talakawa ya kare; ba mai sake tunawa da cewa ai talakawa ne suka zabe shi, sai dai tunanin ya zai yi ya tagayyara talakawa, ya hana su sakat, ya zai yi ya cusa masu bakin talaucin da ba zai bar su su yi tunanin ’yancinsu ba. Sai dai tunanin ya za mu yi mu rayu? Ya zan yi in haddasa gabar kabilanci da ta addini a tsakanin talakawana, don in samu damar sace kudadensu, a yayin da suke can suke karkashe junansu? Wallahi wannan shi ne tunanin wasu shuwagabanninmu a kanmu.
Lallai in dai har za mu san haka, to don me muke barin lokacin zabe yake zama lokacin kakar mutuwa da raunata junanmu? Don me mu ba za mu sama wa kanmu annashuwa, doki da farin ciki a lokutan zabenmu ba? Don me muke barin masu mulki ko masu fatar samun mulki suke amfani da mu don cikar burinsu, su da iyalansu, ba don mu ba? Mu ba mu son jin dadin ne ko mu ba mu son mu zauna lafiya ne? Don me mu ba mu ganin muhimmancin rayukanmu da na ’yan uwanmu? Don me mu ba mu tausaya wa iyalanmu da ’yan uwanmu a halin da sukan shiga idan mun kashe kanmu ko mun aibanta junanmu?
Baya ga wannan ma, ai yana da kyau mu rika tunani da kishin kasarmu. Mu sani ba mu da wata kasa sai wannan, duk wuya duk rintsi ita ce dai abin tinkahonmu. Don haka mu bar barin mutunci da kimarta na faduwa a idon duniya a duk lokacin da aka zo zabe. Abin haushi, har kasashen duniya sun gane da ba mu iya yi wa kanmu adalci a zabe kuma ba mu iya yin zabe cikin lumana. Don lalacewa, har wata kasa ke zuwa tana yi mana kashedin kar mu yarda mu yi zabe marar inganci kuma kar mu yarda mu yi fada bayan zabe. To mu muna ganin kamar ai ba sai an yi mana kashedi ba. Mu ma za mu iya hankaltar da kanmu daga abi da ya faru a baya, mu yi wa kanmu karatun-ta-natsu, mu inganta rayuwarmu, mu sama wa kanmu jin dadi da kwanciyar hankali, mu more ’yancinmu, mu yi wa kanmu galihu. Mu hada kanmu, mu ture bambace-bambancen da ke tsakaninmu, mu tabbatar da canji da ta zarce a inda suka dace da mu.
Daga karshe, ina yi mana nasiha da mu zauna lafiya, mu yi hakuri da junanmu. Allah Ya san dalilin da ya sa Ya yi mu a tare kuma Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so. Mu rika bar wa Allah jagorancin rayuwarmu kuma mu sani duk abin da Ya yi daidai ne, domin Allah ba Ya kuskure.