Zabe: Buhari ya isa Daura don kada kuri’a
Buhari zai kada kuri’a a mahaifarsa a zaben shugaban kasa da ke tafe a ranar Asabar.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina tare da iyalinsa domin kada kuri’a a zaben shugaban kasa da ke tafe ranar Asabar.
Ana sa ran Buhari, wanda ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, zai yi zabe tare da uwargidansa, Aisha da kuma sauran iyalansa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Bangar Siyasa Ka Iya Dagula Lissafi A Wannan Zabe
- ’Yan sanda sun soke duk taron kamfe a Kano saboda rikici
Kafin zuwan Buhari Daura, sai da ya raka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu rufe yakin neman zabensa a Jihar Legas.
Sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ta ce jirgi mai saukar ungulu ne ya kai Shugaba Buhari da iyalansa Daura da misalin karfe 5:25.
Garba Shehu ya ce sanin muhimmancin zabe ne ya sanya Buhari shiryawa tsaf don amfani da kuri’arsa a zaben ranar Asabar.