Zabe: Farashin Kayan masarufi ya tashi a Kudancin Najeriya

Farashin kayan masarufi a Jihar Kuros Riba sun yi tashin gwauron zabi, sakamakon kaurar da ’yan Arewa da ma ’yan asalin makwabtan jihar suka yi zuwa garuruwansu na asali domin gudanar da zaben da za a yi gobe Asabar duk fadin Najeriya. A birnin Kalaba, binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa sakamakon tururuwar […]

Zabe: Farashin Kayan masarufi ya tashi a Kudancin Najeriya
Zabe: Farashin Kayan masarufi ya tashi a Kudancin Najeriya

Farashin kayan masarufi a Jihar Kuros Riba sun yi tashin gwauron zabi, sakamakon kaurar da ’yan Arewa da ma ’yan asalin makwabtan jihar suka yi zuwa garuruwansu na asali domin gudanar da zaben da za a yi gobe Asabar duk fadin Najeriya.

A birnin Kalaba, binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa sakamakon tururuwar da mutanen ke yi domin tafiya kada kuri’a ya janyo tashin farashin. Wakilinmu ya leka Layin Bagobiri, wato unguwar Hausawa da ke Kalaba, inda Malam Ibrahim Musa wani mai sana’ar sayar da kayan abinci ya fada masa cewa, “farashin kayan masarufi sun bambanta kafin zabe ya karato da kuma yanzu da gobe za a yi zaben, domin in ba ka misali da farashin shinkafa ma kadai, abin da ya kawo hauhawar farashinta shi ne saboda faduwar farashin darajar takardar kudin Naira a kasuwar musayar kudi; domin da ita ce suke canja kudinsu, su tafi ketaren kasa su sayo su kawo mana ita nan gida Najeriya. Shi kuma semobita, nasa karin farashin duk da kasancewa abu ne na cikin gida, ya fi cin fuska ga mai saye. Domin a da can muna sayar da shi a farashin Naira 1,750 amma yanzu ya koma Naira 2,000. Gaskiya farashin ya kasance a haka ya yi yawa.” Inji shi.
dan kasuwar yana da kwarin gwiwar cewa bayan kammala zabe, farashin kayan zai sauka duk da kasancewa masu shigo da kayan masarufi daga waje sun bayyana masu cewa sun janye ne domin rashin tabbas na abin da zai biyo baya idan an gama zabe; dole sai komai ya lafa tukuna kafin harkokin su kankama ka’in-da-nain.
Haka kuma Aminiya ta yi kacibis da wani magidanci mai suna Iliyasu Rawayya da ya zo sayen kayan abinci a kasuwar, ya danganta karuwar farashin kayan abinci da tafiya gida da jama’a suka yi domin yin zabe, sannan da kuma matsalar karanci kudi a hannun jama’a.
“karin matsalar ma ita ce, ba kudade a hannun mutane, masu aikin albashi na kukan ba a biya su ba na wasu watanni, sannan kuma ’yan kasuwa na kuka da karancin ciniki saboda babu kudi wadatattu a hannun jama’a.” Inji Rawayya.
Ya karkare da cewa, “Allah Ya hore mana abin da za mu yi hidimar gida da su cikin sauki, dayake cikin kowane tsanani akwai sauki na nan tafe.”
Bayanai da wannan jarida ta tattara daga sauran kasuwanni da ’yan Arewa ke huldar kasuwanci, musamman dabbobi sun nuna cewa an fara samun kamfar dabbobi sakamakon zaben na gobe Asabar, har sai bayan zabe tukuna kafin lamura su daidaita.