Zabe: Jonathan ya fara amfani da ’yan uwansa don kamun kafar sarakuna
A wani sabon yunkuri na gain ya samu karbuwa a yankin Arewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fara amfani da ’yan kabilarsa wajen kamun kafa da rokon masu fada a ji a Najeriya musamman manyan Arewa don su tallafa wajen ganin an sake zabensa.Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida […]
A wani sabon yunkuri na gain ya samu karbuwa a yankin Arewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fara amfani da ’yan kabilarsa wajen kamun kafa da rokon masu fada a ji a Najeriya musamman manyan Arewa don su tallafa wajen ganin an sake zabensa.
Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wata jarida da ake bugawa a Abuja cewa daga cikin sababbin dabarun da Shugaba Jonathan ya bullo da su akwai kai ziyara ga Mai alfarma Sarkin Musulmi da manyan sarakuna da shugabannin addini ciki har da limamai da fastoci da suka fito daga Arewa.
Majiyar ta ce wani babban basarake da wani dan uwan Shugaba Jonathan tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Mukhtari Shagari sun ziyarci Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar a asirce a fadarsa.
dan uwan Jonathan din ya isa Sakkwato ne a jirgin Shugaban kasa, inda kai-tsaye ya zarce fadar Sarkin Musulmi inda suka gana a asirce.
Ba a san abin da suka tattauna a kai ba, sai dai wata majiya a fadar ta ce ziyarar ba za ta rasa nasaba da batun neman a sake zaben Shugaban kasar ba.
Mataimakin Gwamna Mukhtari Shagari dai shi ne ko’odinetan kamfe din Shugaba Jonathan a jihar.
Kuma jaridar ta ce duk kokarin da ta yi don samun karin haske daga jami’an tsaro da ke filin jirgin sama bai samu nasara ba, inda wasu suka ce ba su san da batun ziyarar ba.
Sannan kokarin jin ta bakin fadar Sarkin Musulmin ma bai samu nasara ba, domin wadanda ya kamata a ce sun san da batun ziyarar sun ce ba su da masaniya a kai.