Zabe mai zuwa na cike da ban tsoro – Bolaji Akinyemi
Tsohon Ministan Al’amuran kasashen Waje, Farfesa Bolaji Akinyemi ya ankarar da ’yan Najeriya game da yiwuwar barkewar rikici bayan kammala zabubbukan badi, domin a ganinsa akwai wasu mutane da suke ta kokarin ganin sun haddasa wargajewar kasar.Farfesan ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aika wa ’yan takarar shugabancin kasa biyu na jam’iyyun […]
Muhammadu Buhari, former Nigerian military ruler and presidential candidate for the Congress for Progressive Change (CPC) speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos February 19, 2011. Buhari, the main opposition candidate in Nigeria’s presidential election, said he was optimistic it would be a more credible race than in the past […]

Tsohon Ministan Al’amuran kasashen Waje, Farfesa Bolaji Akinyemi ya ankarar da ’yan Najeriya game da yiwuwar barkewar rikici bayan kammala zabubbukan badi, domin a ganinsa akwai wasu mutane da suke ta kokarin ganin sun haddasa wargajewar kasar.
Farfesan ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aika wa ’yan takarar shugabancin kasa biyu na jam’iyyun PDP da APC, Shugaba Goodluck Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari (ritaya). Ya waiwayi tarihin abin da ya biyo bayan zabubbukan 2011, inda ya ce idan ba a yi hankali ba, abin da zai faru a badi sai ya dara rikicin da ya faru a zaben na baya.
Kamar yadda ya ce: “Ba a dade da nada Mai ba Shugaban kasa Shawara ta fuskar tsaro, Janar Andrew Azazi ba, sai ya bukaci ya gana da ni, inda ya same ni a ofishina domin mu tattauna al’amuran da suka shafi kasa. A lokacin ana gab da gudanar da zaben 2011. Na gaya masa cewa ina cike da damuwa game da wannan zabe…”
A wasikar tasa, ya ce lallai abubuwan da suka haddasa rikici bayan zaben 2011 ba su kai na yanzu ba. “Idan Jonathan ya ci zaben 2015, Arewa za ta barke da rikici, kamar yadda abin ya faru a 2011. Idan kuma Janar Buhari ya ci, Neja-Delta za ta barke da rikici. Wannan batu a bayyane yake, ba mu bukatar wata na’urar kimiyya ta sanar da mu haka.” Inji shi.
Tsohon Ministan ya shawarci ’yan takarar biyu da su hadu wuri guda su rubuta takardar alkawari, cewa za su gudanar da kamfen na lumana, kuma su rika yin kira ga magoya bayansu domin su zauna lafiya, kuma kada su tada hankali a lokutan zabe.
Baya ga ’yan takara, Akinyemi ya roki sarakunan gargajiya da malaman addinan Musulunci da na Kirista, kamar Sarkin Musulmi da Sarkin Kano da sauransu da su shiga cikin shirya taron sasanci da zaman lafiya domin ganin an hada kan kasa, an gudanar da zabubbukan badi lafiya kuma an wanye lafiya ba tare da tashin hankali ba.