Zabe: PDP na shirin yin amfani da makamai – Buhari
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa Jam’iyyar PDP na shirin yin amfani da makamai, sannan ta bai wa wasu mutane kakin ’yan sanda na bogi domin su yi harbe-harbe ta yadda za a soke zaben da za a gudanar a kasar nan gobe. Janar Buhari ya […]
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa Jam’iyyar PDP na shirin yin amfani da makamai, sannan ta bai wa wasu mutane kakin ’yan sanda na bogi domin su yi harbe-harbe ta yadda za a soke zaben da za a gudanar a kasar nan gobe.
Janar Buhari ya shaida wa BBC cewa, “Maganganun da suke zuwa wurinmu sun nuna cewa an sayi makamai a wasu jihohi, an dinka kayan soja da na ’yan sanda da za a bai wa mutanen da aka koya musu harbi; lokacin zabe za su zo su yi harbi domin a ce an yi tashin hankali a soke zaben. Saboda haka duk tsarin da PDP take yi na a soke zabe muna samun labari kuma mu gaya wa ’yan Najeriya.”
Janar Buhari ya bayyana haka ne bayan ganawar da ya yi da masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai wadanda suka kai masa ziyara domin tattaunawa a kan shirye-shiryen zaben na gobe.
Ya bukaci wakilan Tarayyar Turai su dauki mataki a kan batun.
Sai dai a martanin da Jam’iyyar PDP ta mayar kan zargin na Janar Buhari, ta ce zargi marar tushe ne.
daya daga cikin ’yan kwamitin yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan, Alhaji Ja’afar Sani Bello Gamawa ya ce zargin da dan takarar Jam’iyyar APC ya yi, zan ce ne marar tushe. “Wannan zance ne da bai kamata jama’a su saurara ba, saboda Shugaba Goodluck ba ya son fitina, mu ne ke da nasara ba ma bukatar fitina, su ne ba su ga alamar nasara ba, shi ya sa suke neman tunzura mutane,” inji Alhaji Ja’afar Sani Bello Gamawa.
Ya kara da cewa, “Wadannan kalamai na nuna cewa kada jama’a su yarda da ’yan sanda, idan sun gan su, su dauke su a matsayin sojan gona.”