Zabe: Wanda ya ki ji ba zai ki gani ba -Rundunar sojoji

Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Kenneth Minimah ya gargadi cewa duk wanda ya ki ji har ya nemi tayar da husuma a lokacin zabe to ba zai ki gani ba domin zai fuskanci fushin rundunar soja. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani a hedikwatar rundunar sojoji da […]

Zabe: Wanda ya ki ji ba zai ki gani ba -Rundunar sojoji

Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Kenneth Minimah ya gargadi cewa duk wanda ya ki ji har ya nemi tayar da husuma a lokacin zabe to ba zai ki gani ba domin zai fuskanci fushin rundunar soja.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani a hedikwatar rundunar sojoji da ke Abuja shekaranjiya Laraba.
Minimah ya kuma gargadi ’yan siyasar da ke shirin tayar da rikici a lokacin zabe, to inji shi “duk wanda ya ki ji ba zai ki gani ba.”
Za a fara zabe a gobe Asabar inda za a fara da zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya, sannan a yi na gwamnoni da ’yan majalisar jiha a ranar 11 ga Afrilu.
A lokacin da mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Kanar Sani Usman yake bayani ga ’yan jarida ne, Minimah ya isa wajen sannan ya gargadin duk mutumin da ya yi yunkurin tayar da zaune-tsaye.
A lokacin taron wata-wata da rundunar sojoji ta saba yi da ’yan jarida ne Kanar Usman ya rika amsa tambayoyin ’yan jarida, inda na wannan karon aka shirya shi don zabe da ke tafe, sai Minimah ya shigo wurin, sannan aka ci gaba da yin taron da shi.
Ya ce: “Duk wanda yake yunkurin tayar da husuma ko rikici a lokacin zabe, to zan sanar da shi idan ya ki jin gargadin da za mu yi masa, to ba zai ki gani ba, muna nan muna jiransa.”
Ya ce a shekarun baya Barack Obama da Mitt Romney sun yi takarar shugabancin kasar Amurka a jam’iyyu daban-daban, inda kowa a cikinsu yake da dimbin magoya baya, amma babu wanda ya nemi yi wa zaman lafiyar kasar barazana, ko ya yi barazanar tayar da rikici.
Janar Minimah ya ce babu wata jam’iyyar da ta shiga zabuka a Birtaniya da ta yi yunkurin tayar da zaune tsaye. “Babu wanda yake tunanin rikici a matsayin hanyar cin zabe, me ya sa mu a Najeriya muke amfani da tayar da husuma a lokacin zabe?”
“Don haka ya kamata kowane dan Najeriya ya je rumfunan zabe cikin salama, ya jefa kuri’a sannan ya shiga harkokinsa na yau da kullum. Duk wanda ya nemi tayar da rikici, zai hadu da gabansa, ya kamata a yi zabe lafiya, idan ka samu nasara ka yi mulki, idan ka rasa kana tunanin an yi magudi, to ka nufi kotu.” Inji shi.
Janar Minimah ya roki ’yan siyasa su ja kunnen magoyan bayansu da masoyansu cewa su guji tayar da rikici a lokacin zabe, sannan su tabbatar da zaman lafiya.
“Ina kira ga ’yan Najeriya masu bin doka da oda da su fita kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri’arsu ga duk dan takarar da suke so ba tare da tsoro ko fargaba ba, ’yancinsu ne su kada kuri’a.”
Ya kara da cewa sojoji da sauran jami’an tsaro sun shirya tsaf don samar da tsaro a lokacin zabe.
A dangane da hukuncin da kotu ta yanke da ya hana amfani da sojoji lokacin zabe sai Minimah ya ce: “Zan kara yi fashin baki a kan wannan hukunci, ba wannan ne lokaci na farko da za a fara gudanar da zabe a kasar nan ba, kun ga yadda aka gudanar da zabubbuka a Najeriya, kun kuma ga yadda sojoji suka samar da tsaro a lokacin zabubbukan. Kun taba ganin sojoji a rumfunan zabe? Kun taba ganin sojoji suna kirga kuri’un da aka kada? Ko sukarike kuri’u, ko akwatunan zabe, ko wani abu na kayan zabe? Don haka ban san me kuke magana a kai ba? Ya kamata ma in tambaye ku ne.” Inji shi.