Zaben 2015: Hadarin da ke cikin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (2)

Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA), ya ce; “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce wa Ka’ab bin Ujrata (RA): “Allah Ya tsare ka, Ya kiyaye ka, ya kai Ka’ab daga riskar shugabancin mutanen banza, jahilai wawaye; sai Ka’ab ya ce: “Mene ne shubagancin mutanen banza, wawaye ya Manzon […]

Zaben 2015: Hadarin da ke cikin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (2)
Zaben 2015: Hadarin da ke cikin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (2)

Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA), ya ce; “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce wa Ka’ab bin Ujrata (RA): “Allah Ya tsare ka, Ya kiyaye ka, ya kai Ka’ab daga riskar shugabancin mutanen banza, jahilai wawaye; sai Ka’ab ya ce: “Mene ne shubagancin mutanen banza, wawaye ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce: “Wasu shugabanni ne da za su zo nan gaba, ba sa bin shiriyata, kuma ba sa bin tafarkina. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyarsu kuma ya taimake su a kan zaluncinsu, to ba ya tare da ni, kuma ba na tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyarsu ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to wadannan suna tare da ni, kuma ina tare da su, sannan za su sha ruwan tafkina.” Annabi (SAW) ya ci gaba da cewa:”Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, Sallah neman kusanci ne zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce. Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haram, to har abada ba za ta shiga Aljanna ba, kuma wuta ita tafi cancantarta. Ya Ka’ab bin Ujrata! A kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da rayuwarsa, akwai wanda zai ’yanto ta, ko ya halakar da ita.” (Ahmad da Bazzar suka ruwaito)
Ya ku mutane! Ku sani, shi mutumin banza, jahili, shi ne mai karancin hankali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, ba zai iya shugabantar iyalinsa ba, balle ya shugabanci waninsa. To ’yan uwa, irin wannan mutum yaya za a yi ya shugabanci sama da mutum miliyan 170? Idan ’yan kasa sun yi sakaci zai yi, amma kasar za ta susuce, ta tabarbare ta lalace!
A wani Hadisin, Annabi (SAW) y ace: “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai ya kasance munafukan cikin al’umma da wawayenta su ne za su yi shugabanci.” (dabarani ya ruwaito).
Munafukai da wawaye za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, barayi, marasa tausayi, wadanda kansu kawai suka sani, sai ’ya’yansu da iyalansu da abokansu. Babu ruwansu da sha’anin talakawa da al’umma.
Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai idan aka wayi gari masu mulkin mutane, wato shugabanninsu ko jagororinsu, sun kasance ashararai, mutanen banza, jahilai, wawaye, to, lallai al’amarinsu zai lalace! Sai a wayi gari ana girmama mutanen banza a gwamnati, ana wulakanta mutanen kirki. A yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana, sai ya kasance jahilai, marasa mutunci, tsageru, ’yan ta’adda da suka kware wajen iya cuta da magudi da sharri sune masu fada-a-ji a gwamnati. Masana dattawa mutanen kirki ba su da bakin magana, ko sun yi ba ta da tasiri da matsayi a wurin gwamnatin, saboda gwamnati ce ta ’yan iska, gwamnati ce ta barayi, ’yan ta’adda, mashaya jinin dan Adam, ’yan giya, marasa mutunci!
Babban malami Imamu Sha’abiy (Allah Ya rahamshe shi) yana cewa; “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallonsa jahilci, jahilci kuma ana kallonsa ilimin.” Wannan duk zai faru ne a cikin wannan zamani da al’amura suka birkice, suka lalace, suka rincabe aka rasa shugabanni nagari.
Kuma Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa: “Lallai yana daga alamomin kusantowar Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.”  (Al-Hakim ya ruwaito a Al-Mustadrak).
Ya ku ’yan Najeriya! A yau duk wanda yake raye shaida ne a kan cewa lallai duk abin da Annabi (SAW) ya ba da labari shi ne ke faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantarmu ashararai ne, sai fa ’yan kadan daga cikinsu. Saboda duk yadda al’amari ya kasance ba a taruwa a zama daya, kuma ba a rasa na kirki a cikin shugabanni. Sannan ya zama wajibi a gare mu kowa ya yi kokari ya ba da gudunmawa gwargwadon ikonsa, don ya zama wadanda za su shugabancemu a nan gaba, (musamman a zaben 2015) mutanen kirki ne.
’Yan uwana ’yan Najeriya! Mu sani, wallahi lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba a ce mutanen banza ke jagorantarmu. Mu sani, dukkanmu Allah (SWT) zai kama mu da laifin rashin tabuka komai, a kan samar wa al’umma nagartattun shugabanni. A yau dukkanmu shaidu ne kan irin halin da kasarmu mai da yankinmu mai albarka na Arewa suka shiga, saboda rashin shugabanci nagari. To abin da ya faru ya riga ya faru, yanzu abin tambaya shi ne; me muke yi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai, masu amana? Ko har yanzu barci muke yi ba mu farka ba?
Ya ku bayin Allah! Mu sani, lallai asalin shugabanci shi ne; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da lafiya da rashin nuna bambanci ga ’yan kasa, mai kokarin hada jama’ar kasa da rashin son kai, mai kishin kasa kuma gogagge, gwarzon namiji, jarumi da sauransu. To amma a yau abin ba haka yake ba, domin fasikai, mutanen banza, ashararai, mayaudara, mashaya, barayi, wadanda ba su san kimar dan Adam ba, ke shugabantarmu. Saboda suna da kudi, ko don dangartakarsu, ko wani matsayi da suke da shi, ko saboda tsabagen rashin kunyarsu, ko don ’ya’yan manya, amma ba don cancanta ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko saboda mutanen kirki sun yi saranda, sun rungume hannuwa, sun zama matsorata, sun mika wuya, sun ce su babu ruwansu da siyasa, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.
Ya ku ’yan Najeriya! Awfu bin Malik ya ruwaito Hadisi cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafifitan shugabanninku su ne wadanda kuke kauna, kuma suke kaunarku, kuke yi musu addu’ar alheri, su ma suke yi muku. Sannan mafi lalacewar shubaganninku, su ne wadanda kuke fushi da su, suke fushi da ku, kuna la’antarsu, su na la’antarku.” (Muslim ya ruwaito).
Saboda haka ya ku al’umma! Wallahi ya zama wajibi a gare mu, manyanmu da shugabannin siyasarmu da sarakunanmu da shugabannin addinanmu da manyan masu kudinmu da ’yan kasuwarmu da ’yan bokonmu da talakawanmu da jami’an tsaronmu da ’yan jaridarmu da duk wani mai ruwa da tsaki a game da samar da shugabanci nagari a kasar nan, mu hada hannu da karfi mu ga cewa lallai wannan kasa tamu mai albarka Najeriya, ta samu shugabanci nagari.
Idan ba haka ba kuwa, wallahi dukkanmu Allah zai kama mu da laifin yin sakaci, gobe kiyama.
Saboda haka mu ji tsoron Allah! Ya ku muminai mu koma ga Allah!  Mu nemi kusancin Mahaliccinmu ya ku mutane! Mu roki Allah shiriya da tabbatuwa a kan gaskiya, mu tuba zuwa ga Allah baki daya ya ku muminai! Ko ma samu rabauta.
Ya Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka taimaki Najeriya da ’yan Najeriya, Ka taimake mu da shugabanni masu tsoronKa, Ka kaskantar da kafirci da kafirai, Ka halakar da makiyanKa makiya addininKa, marasa kaunar zaman lafiya, Ka taimaki bayinKa salihai masu gaskiya a duk inda suke, Ka ruguza gungun munafunci da munafukai.