Zaben 2015: Limaman coci sun juya wa Jonathan baya

Ga alamu an samu mummunar baraka tsakanin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan da wasu daga cikin limaman coci sakamakon nuna gazawarsa da suka rika yi na mulkin kasar nan.Limaman cocin sun rika fitowa daya bayan daya suka rika sukar yadda shugaban yake gudanar da mulki.Wasu daga cikin limaman cocin sun fito karara sun nemi da ya […]

Zaben 2015: Limaman coci sun juya wa Jonathan baya
Zaben 2015: Limaman coci sun juya wa Jonathan baya

Ga alamu an samu mummunar baraka tsakanin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan da wasu daga cikin limaman coci sakamakon nuna gazawarsa da suka rika yi na mulkin kasar nan.
Limaman cocin sun rika fitowa daya bayan daya suka rika sukar yadda shugaban yake gudanar da mulki.
Wasu daga cikin limaman cocin sun fito karara sun nemi da ya yi murabus daga kan karagal mulki.
Limamin da ake ganin shi ne ya fara fitowa fili ya soki Jonathan din shi ne Rabaren Ejike Mbaka, shugaban cocin Adoration Ministry da ke Enugu inda a wani wa’azi da ya yi wa dimbin magoya bayansa a karshen shekara ya nemi Jonathan da ya yi murabus.
‘Ci gaba da mulkin Jonathan bala’i ne ga ’yan Najeriya domin ya gaza a bangarori da dama saboda haka ba zai iya mulkin kasar nan ba. Darajar kudinmu ta karye babu wuta babu kyawawan hanyoyi ga tsananin rashin tsaro har yanzu ’yan matan da ’yan boko haram suka sace ya kasa dawo da su, cin hanci ya yi yawa babu aikin yi ga dimbin wadanda suka kammala karatu, ai ita kan ta boko haram da garkuwa da mutane danjuma ne da danjummai da rashin aiki yi. Saboda haka nake kira a gare shi da ya sauka daga kan mulki ya baiwa wanda zai iya jan ragamar kasar nan kamar Janar Buhari’.
Rabaren Mbaka wanda ya ci gaba da cewa ‘Har nan aka kawo mani matar shugaban kasa Patient Jonathan domin na yi wa mujinta addu’a. Na ummar ce ta da ta zo mani da tantabaru guda hudu. Uku suka tashi amma dayan da ya fi lafiya wanda shi ne na Jonathan ya ki tashi. Muka yi iya kokarinmu ya tashi amma ya ki tashi daga bisani sai aka sanar da ni cewa mu hakura ba zai tashi ba domin shugaban kasa ya gaza ba zai iya mulkin kasar nan ba’.
Limamin cocin da ya biyo bayansa shi ne shugaban cocin Latter Rain Assembly da ke jihar Legas, Fasto Tunde Bakare inda shi ma a sakonsa na karshen shekara ya nuna gazawar gwamnatin Jonathan.
Fasto Tunde ya ce ‘A karkashin Gwamnatin Jonathan komai ya tabarbare mutane suna cikin mawuyacin hali, tattalin arziki ya lalace darajar kudinmu ta fadi, babu aikin yi, babu abubuwan more rayuwa; babu kwanciyar hankali; al’amuran tsaro sun lalace mutane sun shiga rudani. Saboda haka nake kira ga jama’a su zabi wanda suke ganin zai yi musu aiki’.
Limamin coci na uku, shi ne, fitattacen limamin nan mai suna Fasto Peter Ayegun na Jihar Legas, wanda ya bayyana cewa ya gano cewa Shugaba Jonathan ba zai ci gaba da mulki ba.
Ya ce ‘Na gano cewa jam’iyyar PDP da Shugaba Jonathan ba za su ci gaba da mulkin kasar nan ba. A zabe mai zuwa PDP  za ta rasa mafi yawan jihohin da take da su ga jam’iyyun adawa. Jihohin kuwa sun hada da Legas da Kano. “Jam’iyyar PDP ba za ta iya lashe zabe ba daga jihohin sai dai a jihar Legas PDP za ta iya bayar da mamaki idan ta yi wasu gyare-gyare” a cewarsa.
Sai dai a martanin da jam’iyyar PDP ta mayar, ta yi watsi da maganganun da limaman cocin suka yi, inda ta yi zargin wasu daga ciki sun karbi cin hanci don su bata wa Jonathan da jam’iyyar suna.
daya daga cikin shugabannin jam’iyyar Barista Jalo, ya bayyana cewa ‘Ai shi dama Rabaren Mbaka ba yau ya fara irin wannan abin ba. Duk lokacin da aka ce limamin coci ya kauce daga matsayinsa ya koma siyasa to babu shakka mabiyansa za su yi masa tawaye. Ta yiwu kudi aka ba shi domin ya bata wa jama’a suna’.