Zaben 2015: Za a gudu ne ba za a tsira ba

Ingantaccen zabe ne kashin bayan dimokuradiyya a kowace kasa. Shi ne ke share fagen kafuwar gwamnati da kuma kafa ginshikan adalci da kamanta gaskiya a harkokin mulki. Zaben da aka yi shi bisa tsarin da ya dace ne ke kwantar da hankulan jama’a har su kasance masu biyayya sau da kafa ga shugabannin da hakan […]

Zaben 2015: Za a gudu ne ba za a tsira ba
Zaben 2015: Za a gudu ne ba za a tsira ba

Ingantaccen zabe ne kashin bayan dimokuradiyya a kowace kasa. Shi ne ke share fagen kafuwar gwamnati da kuma kafa ginshikan adalci da kamanta gaskiya a harkokin mulki. Zaben da aka yi shi bisa tsarin da ya dace ne ke kwantar da hankulan jama’a har su kasance masu biyayya sau da kafa ga shugabannin da hakan ya haifar. To amma a Najeriya ba haka nan al’amarin ke kasancewa ba. Akasin abin da ake kira dimokuradiyya, watau mulkin kama-karya ke wanzuwa, yayin da talakawa ba su da ta cewa a harkokin yadda ake gudanar da mulkin da ya shafe su, duk kuwa da cewa  kuri’unsu ne ikonsu na kafa gwamnatin da za ta share masu hawaye, ta kuma biya masu dukkan bukatunsu.
A dukkan lokutan da aka ce za a yi zabe  to hayaniya da tankiya ba za su kare ba, kuma  bayan an gudanar da zaben  bacin rai da tashin hankali za su biyo  sakamakonsa, su kuma dade suna ci wa jama’a tuwo a kwarya. Abin takaici game da haka shi ne an kasa gano dalilan da ke hadasa haka, an kuma kasa kago dabarun illolin da suke haddasawa. A takaice dai ana iya cewa babban abin da ke tayar da zaune-tsaye, yake kuma haddasa husuma da tashin-tashina a kasar nan bai wuce batun zabe da matakan siyasar da ake bi a kai gare shi ba.
A yanzu ma ko da Hukumar Zabe ta kasa, watau INEC a Turance, ta bayyana cewa za a kwance wa ‘yan siyasa dabaibayi a watan Satumbar wannan shekarar don fara fafatawa a yakin neman zaben shekarar 2015, babu abin da ya canja game da halayyar ‘yan siyasa da kuma dangantakarsu da jam’iyyunsu. Wannan al’amari bai dada su da kasa ba, bai kuma burge su ba, domin su tuni sun rigaya sun kintata yanayin da za su bi don yakin neman zabe da kuma irin wainar da za su tottoya a ranakun zaben  ba tare da jiran umurnin haka daga hukumar zaben da wasunsu suka dunkule, suka jefa a aljihunsu ba.
Halayya da take-taken ‘yan siyasa sun tabbatar wa jama’a cewa ko da hukumar zabe, ko babu ita za su yi ta kulle-kullen da suka saba, a asirce ko a bainal-jama’a wajen share fagen tsayar da dan takara, za su kuma yi ta wadaka da dukiyar sata don saye jama’ar da za su ba shi goyon baya a fakaice ko kuma a kaikaice, illa kawai su jira lokacin da hukumar zaben za ta ce su fito, su  a zahiri don tabbatar da  abin da abin da suka kitsa a badini, yayin zabubbukan fitar da gwanaye. Wannan shi ne hakikanin abin da zai faru, abin da kuma ‘yan siyasa suka jira ke nan, ba kuma abin da ya dame su da tunanin talakawa na daukar matakan yin gyararrakin ga harkokin zabe don guje wa  matsalolin gidan jiya da ke hana shi armashi.
Bisa ga dukkan alamu gwamnati da hukumar zabe ba su tunanin haka, hankulansu sun zarme kan mara wa juna wajen dakile burin jama’a da kuma yadda za su sake dasa miyagun shugabannin da za su ci gaba da gallaza wa talakawa, suna kyautata wa kawunansu da iyayen gidansu na nan cikin gida da kuma na ketare don su ji dadin tatse kasar karkaf, su bar ta ba ko karfanfana. Akwai gyararraki birjik da za a yi don share fagen wanzuwar zabe ingantacce da zai biya bukatun talakawa,  musamman ta fuskokin tsara shi da kuma yadda za a gudanar da shi da la’akari da abubuwan da za su biyo bayansa.
Alal misali ita kanta hukumar zaben akwai ayar tambaya akanta game da ingancin shugabanninta da kuma yadda ake nada su kan mukamansu. Baicin haka nan kuma akwai batun kafa hukumar hukunta masu aikata magudin zabe da yin kwaskwarima ga dokokin da ke kawo cikas wajen sauraron kararrakin zabe da kuma magance matsalolin da ke kawo cikas game da gudanar da zaben kamar rashin ingantacciyar rajista da kuma dogon jinkirin da ake samu kafin akai kayayyakin aiki tashoshin jefa kuri’a da kuma yadda akan kai muhimman kayayyaki wasu wurare a ki kai wa wasu.
Bayan wadannan abubuwan takaicin da kan rage wa harkokin zabe armashi akwai kuma halayyar shugabannin gwamnatoci da ‘yan siyasar da ke masu ingiza-maikantu-ruwa, wadanda kan tayar da yamutsin da zai hargitsa al’amura a ranakun zabe. Idan har sun fahimci cewa nasara ba ta gefensu, to za su kifar don kowa ya rasa. Haka nan su ma shugabanni masu jan ragamar gwamnatoci kan hada baki da hakiman tsaron da ba su tsoron Allah don yin murdiya da munakisar da ke haddasa gagarumar fitina.  A halin yanzu dai  ana iya cewa ‘yan siyasa ba su mance da miyagun dabi’unsu ba, ba su kuma koyi darasin komai ba daga masifun da suka jawo wa jama’a. Abin tsoro game da haka shi ne za a koma gidan jiya ne idan aka zo zaben 2015, domin kuwa ga shin tun daga yanzu bakin burin wasu manyan ‘yan siyasa na haddasa tsananin rudani da kara rarraba kawunan jama’a bisa akidar kabilanci da bambancin addini. Muddin ba namijin kokari ne ba ka yi don kawar da batun addini a harkokin zabubbuka masu zuwa, to za a gudu ne kawai amma ba za a tsira ba.