Zaben 2019: Akwai bukatar iyaye da sarakuna da malamai su fadakar da jama’a

Assalam Edita, iyayenmu malamai da sarakuna da sauran jagororin jama’a. Da fatan za ku kara kaimi sosai wajen fadakarwa da nuna wa jama’a muhimmancin yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Da kuma nuna masu illolin da tayar da zaune-tsaye ke haifarwa ga jama’a da kasa baki daya. Da fatan za mu yi zabubbukan da […]

Zaben 2019: Akwai bukatar iyaye da sarakuna da malamai su fadakar da jama’a
Zaben 2019: Akwai bukatar iyaye da sarakuna da malamai su fadakar da jama’a

Assalam Edita, iyayenmu malamai da sarakuna da sauran jagororin jama’a. Da fatan za ku kara kaimi sosai wajen fadakarwa da nuna wa jama’a muhimmancin yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Da kuma nuna masu illolin da tayar da zaune-tsaye ke haifarwa ga jama’a da kasa baki daya. Da fatan za mu yi zabubbukan da ke gabatowa cikin kwanciyar hankali da lumana.

Daga Shugaban Kungiyar MURYAR JAMA’A Haruna Muhammad Katsina. 07039205659

 

Kira ga shugaban karamar hukumar Gwarzo

Salam Editan AMINIYA. ina so ka taimake ni in mika rokona ga Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo da ya yi wa Allah da Annabi ya gyara wutar lantarkin garin Sabon Layin Kara.

Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Shu`aibu Sabon Layin Kara, Gwarzo Inkiya Mile!2 Legas 09023489162.

Sakon ta’aziyya ga al’ummar Nasarawar Kaduna

Assalamu alaikum Editan jaridar AMINIYA mai albarka. Don Allah ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyya ga al’ummar Nasarawa da sabon garin Nasarawa da iyalai da ’yan uwan marigayi Limamin Masallacin Juma’a na Nasarawa Kaduna, Liman Isma’il Muhammad wanda ya kwanta dama ranar Alhamis 24 ga Janairu 2019, Allah Ya jikansa da rahamarSa amin ya Allah.

Daga Aminu Salisu Sarauta Dirkaniya Kaduna  08060707685.

Kira ga Shekarau da Kwankwaso

Assalam Edita. Ina kira ga Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kwankwaso a kai zuciya nesa. Duniya ce, kada na baya su yi koyi da halin da kuke ciki a halin yanzu da muke ciki na siyasa. Daga na gaba ake gane zurfin ruwa.

Daga Ibrahim Dankoli Jada Adamadwa  07034542318.

’Yan Najeriya kada ku yi sakaci a zabe

Taka kafar da kaza take yi wa danta ba niyyar kisa ba ne gyara ne. Da taimakon Allah kada a yi sakaci wajen zaben Shugaba Muhammadu Buhari. Mun fada gwamnatinmu ta APC ce, daga kansila har Shugaban Kasa a Najeriya APC ce, dalili wallahi in wata jam’iyyar ce ke da mafi rinjaye to APC me za ta samu? Wannan dalili ya sa da irin tukunyar da suka dafa mu shekara 16, mu ma mu dafa su na shekara 26, wannan shi ne manufata. Ko su sun tabbata Baba Buhari mai adalci ne, ya zama amintacce a gun duk dan Najeriyaa.

Daga Usman Magaji Kalgwai, Karamar Hukumar Auyo Jihar Jigawa 08063437074.

Ga sabon Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya

Assalam Edita. Ka ba ni fili in yi godiya ga Allah, in yi murna da rawa da shewa da jinjinar ban girma da mubaya’a da addu’a ga sabon Sufeto Janar ’Yan sandan Najeriya, Dattijo Abubakar Adamu kan tabbacinmu na zai kawo cikakken tsaro a kasa. Kuma ganin kwararre ne kan aikin dan sanda mun san zai canja akalar aikin zuwa tafarkin da zai yi daidai da na ’yan sandan duniya. Mun tabbata zai shimfida adalci a gidan ’yan sanda, muna rokon ya fara da biyan dukan hakkin ’yan sanda musamman wadanda suka rasu a bakin aiki. ’Yan sanda kalubalenku, ga ku ga sarkin aiki, Dattijo wargi babu.

 Daga Amiru Bakori, 08084213547.

Tambaya ga Gwamnatin Buhari

Wai jita-jitar da mutane ke fadi gaskiya ce, cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta bai wa ’yan takara kudin da kowace gwamnati ke bayarwa ba. Idan haka ne gaskiya Mai girma Shugaban Kasa bai yi wa jam’iyyu adalci ba, kada ya manta duk takarar da ya yi a baya, sai da Gwamnatin Tarayya a lokacin ta ba shi kudin da zai yi kamfe. Idan ya yi haka ya karya dokar kasa da ta ba da damar yin haka? Me zai ce ga ’yan Najeriya idan shi ya zama mai karya dokar kasa?

Daga Jamila A Muhammad Fagge, Kano

 

Kira ga ’yan siyasar Najeriya

Assalamu alaikum Edita. ’Yan siyasa sanin shekaran jiya da jiya, shi ke gyara yau don a ci moriyar gobe da jibi.

Daga Usman Bala {Ninja} Kagoro 07037084451.

Ya kamata Gwamnati ta kyale CJN ya ci gaba

Assalam Edita, kamar yadda wadansu mutane suka yi ta babatu a kan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar cewa, ba zai iya zuwa kasar Amurka ba, kuma tunda ya shirya ya tafi shi kenan sai babatu ya kare. Shin me zai hana shi ma shugaba Buhari ya kyale Babban Joji ya ci gaba da gudanar da harkokinsa domin kawo karshen takaddamar da ake yi a tsakanin al’umma a yanzu?

Daga Abdul’aziz A’nu Maska Funtuwa 07039117305.

 

Mene ne alakar PDP da Babban Joji?

Assalamu alaikum jaridar AMINIYA mai albarka. Allah Ya kara muku kaifin basira da hazaka amin. Ina so in yi amfani da wannan dama in tambayi mambobin Jam’iyyar PDP game da hutun da suka bai wa kansu na yakin neman zabe don dakatar da Babban Jojin Najeriya. Muna so su yi mana bayanin mece c e alakar su da shi? Ko sun kulla wata manakisa da shi ne don yin magudin zabe? To an yi walkiya mun gan ku.

Daga Lamido Ahmadu Danlami Biu, Borno 08026699447.

 

Ta’aziyya ga mazauna Mil 12

Assalamu alaikum Editan jaridar AMINIYA mai albarka. Don Allah ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyyata ga al’ummar Mil 12 mazauna Legas da kuma ’yan uwa da iyalan marigayi Alhaji Yahuza, Shugaban Kasuwar ’Yan tumatir na Kasuwar Mil 12. Allah Ya jikansa da rahama Ya sa mutuwa ta zamo masa hutu Ya kuma bai wa iyalansa hakurin rashin.

Daga Muhammadu Tasi’u M. Sani Argungu mazaunin Oshodi Jahar Legas 08062236122.

 

Jinjina ga matasan Kura

Assalam Edita. Don Allah Editan Aminiya ka ba ni fili in dan yi bayanin a kan yadda matasan Rigar Duka da ke Karamar Hukumar Kura a Jihar Kano suka kama wani mai lalata musu yara ranar Asabar 26 ga Janairu 2019. Gaskiya sun burge ni yadda suka natsu, ba hayaniya bayan ya fara lalatar suka kulle kofar sannan suka tara mutane kowa ya gan shi. Yanzu dai yana hannun ’yan sandan ofishin Kura, inda za su mika shi ga kotu don ya girbi abin da ya shuka, Allah Ya tsare mu, amin.

Daga Husaini Tsoho Imawa Kura 08165610365.

 

Kira ga matasa kan zaben 2019

Assalam Edita. Ina son ka ba ni dama domin in yi kira ga ’yan uwana matasa a kan zaben da ke tafe. Ya kamata mu tsaya mu yi tunani kada mu yarda a yi amfani da mu wajen yin magudin zabe ko ta da fitina. Kuma ya kamata mu yi koyi da siyasar kasashen da suka ci gaba duk mutumin da muka san zai yi mana adalci to ko a wace jam’iyya yake mu zabe shi. Lokaci ya yi da za mu bar siyasar jam’iyya murika yin siyasar mutum saboda a gaskiya yanzu a Najeriya siyasar jam’iyya sam ba ta da wani amfani don haka kada mu yarda ’yan siyasa su yi mana yaudara irin ta zaben 2015 Allah Ya sa mu gane amin.

Daga Hadi Tsohon Sarki Daura-08164205067-08136433609.

 

Sake zaben Gwamna Bello Masari alheri ne

Assalam Edita. Hakika sake zaben Gwamna Aminu Bello Masari a karo na biyu a zabe mai zuwa shi ne mafi alheri gare mu Katsinawa. Ganin rawar da ya taka a duk mukaman da ya rike kafin zamansa Gwamna ya fi duk wadanda ke neman kujerar a yanzu. Kuma ko a Gwamnan da ya rike a yanzu ya taka rawa sosai, idan Katsinawa suka rasa shi zai wuya a samu kamarsa. Fatarmu Allah Ya maimaita mana a 2019, amin.

Daga Usman Manika Mairuwa Road Funtuwa 080609856

 

Kira ga matasa kan shafukan sadarwar zamani

Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya mai albarka. Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga ’yan uwana matasa masu amfani da kafafen sadarwa na zamani cewa ya kamata mu sani malamai fa su ne fitilar al’umma, don haka ya kamata mu yi taka tsantsan mu daina cin mutuncinsu da sunan siyasa, domin neman daukaka a wajen ’yan siyasa.

Daga Aminu Adamu Malam Madori, Jihar Jigawa, 08182315298.

Sakon ban-gajiya ga ’yan Kungiyar RAYAAS

Salam Editan Aminiya. Don Allah  ku mika mana sakon ban-gajiya ga Shugabanin Kungiyar Rayuwarmu A Yau ta Kasa (RAYAAS) kan taron da suka gudanar a Jihar Kano, Allah Ya huta gajiya Ya sa kuma alheri a ciki.

Daga Shugaban Kungiyar RAYAAS ta Jihar Yobe Alhaji Umar Foreber Gashuwa 08108003333.

 

Kashenmu zai bushe idan Buhari ya zarce

Kowa ya san cewa idan har gwamnatin Baba Buhari ta sake cin zabe a karo na biyu to kashinsa ya bushe.

Daga Yakubu (Kurma) Maigidan Gona Unguwar Kaya Zariya 08149454672.