Zaben 2019: APC ba tada dan takarar Gwamnan Zamfara – Kotu
Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Sakkwato ta soke hukuncin wata babbar kotun Zamfara da ta bai wa jam’iyyar APC damar tsayar da dan takara a zaben Gwamna da aka kammala. Rahotan na bayyana cewa, zaman kotun daukaka karar a birnin Sakkwato a yau Litinin, karkashin jagorancin Mai Shari’a Tom Shuaibu Yakubu, […]
Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Sakkwato ta soke hukuncin wata babbar kotun Zamfara da ta bai wa jam’iyyar APC damar tsayar da dan takara a zaben Gwamna da aka kammala.
Rahotan na bayyana cewa, zaman kotun daukaka karar a birnin Sakkwato a yau Litinin, karkashin jagorancin Mai Shari’a Tom Shuaibu Yakubu, ya soke hukuncin kotun ta Zamfara akan, katun ba tabi hujjoji kwarara ba wajen yanke hukuncin.
A cewar alkalin bayan binciken da kotun ta yi, jam’iyyar APC ba tayi amfani da dokokin hukumar zabe wajen zaban dan takara ba.