Zaben 2019: Ba mu da dan takara sai Sule Lamido – Alelu

Wata kungiyar siyasa ta Credible Alternatibe ta kasa reshen Jihar Kebbi ta bayyana cewa zabe mai zuwa na shekara 2019, ba ta da dan takarar shugaban kasan da ya wuce Dakta Sule Lamido a karkashin Jam’iyyar PDP don Najeriya ta samu tafiya kafada da kafada da manyan kasashen da suka cigaba ta fuskar tattalin arzikin […]

Zaben 2019: Ba mu da dan takara sai Sule Lamido – Alelu

Wata kungiyar siyasa ta Credible Alternatibe ta kasa reshen Jihar Kebbi ta bayyana cewa zabe mai zuwa na shekara 2019, ba ta da dan takarar shugaban kasan da ya wuce Dakta Sule Lamido a karkashin Jam’iyyar PDP don Najeriya ta samu tafiya kafada da kafada da manyan kasashen da suka cigaba ta fuskar tattalin arzikin kasa da wanzuwar dimokuradiyya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Halliru Alelu ne ya bayyana haka a lokacin da suka gudanar da wani babban taro a Birnin Kebbi, inda ya ce, “Dakta Sule Lamido ya rike muhimman makamai a baya kuma baya da tsoro wanda ya goge akan fannoni daban-daban na harkar siyasa da lamurran kasa da iya mulki. 

Kuma kowa ya san yadda jihar Jigawa take kafin Sule ya zama gwamna babu jihar da ba ta fi Jigawa ba, amma yanzu Jigawa ta wuce tsara zuwan Lamido, kuma kowa ya san Dakta Sule lamido ya rike mukamai har guda tara, ya fara tun daga kujerar dan majalisar tarrayya Legas har zuwan zaman shi Gwamna babu inda ya sami nakassu a aikin shi kuma ba shi da wari a siyasance a yanzu a Najeriya wanda ake yi da shi a yanzu sai Lamido.”

Alelu ya ce, kungiyarsu ta Credible Alternatibe, wanda take karkashin PDP kuma take da rassa a dukkan jihohin kasar nan, an kafa ta ne da muradin kawo canji mai nagarta a kasar nan. Kuma ya ce, “Mu ‘ya’yan wannan kungiya mun ga ya zama wajibi a garemu da mu mara wa Dakta Sule Lamido baya, don neman shugabancin kasar nan a zaben 2019, kwarewarsa da iya siyasa, shi ya sa muke ganin idan har ya samu mulkin Najeriya zai iya hada kan ‘yan kasar baki daya, kuma mutum ne mai rikon amana da tsaya wa akan gaskiya,” in ji shi.