Zaben 2019: Baba kar a yi SAK!

Zaben shekarar dubu biyu da sha biyar (2015) da ta gabata idanun mutane ya rufe, sun makance kawai ganin duk wanda yake a PDP ake a matsayin hamshakin azzalumin da ya hana talakawa samun ingantacciyar rayuwa. Wannan ne ya sanya mutane da dama suka fusata don ganin an kawar da ita daga mulki, tare da […]

Zaben 2019: Baba kar a yi SAK!

Zaben shekarar dubu biyu da sha biyar (2015) da ta gabata idanun mutane ya rufe, sun makance kawai ganin duk wanda yake a PDP ake a matsayin hamshakin azzalumin da ya hana talakawa samun ingantacciyar rayuwa.

Wannan ne ya sanya mutane da dama suka fusata don ganin an kawar da ita daga mulki, tare da kyautata wa Jam’iyyarmu ta APC kyakykyawan zaton sama wa talaka hanyar da zai samu saukin rayuwa. A hannu daya kuma hakan ne ya bada damar zaben dukkanin wanda APC ta tsayar ba tare da la’akari da kyawun hali ko munin halinsa ba.

A wancan lokacin talakawa sun bi umarnin Baba Buhari na cewar a yi Sak,an kuma yi sak din don kara jaddada soyayyar da ake masa,wanda a halin yanzu Sak din take aiki a kan Talaka yake ganin Cak!

Bugu da kari an yaudari mafi yawan talakawa da cewar su zabi APC daga sama har kasa domin samawa Baba Buhari abokan aiki wadanda ba za su ba shi matsala ba a kan kudurorinsa na son dora Najeriya a bisa kyakkyawar turba. 

Amma sabanin hakan sai ga shi wadanda aka zaba da niyyar su taimaka masa su ne suka dawo suke cin dudduniyarsa,suna dakile dukkan wani kuduri da zai sanya talaka cikin sa’ida. Su ne a sahun gaba wajen gasa wa talaka tsakuwa a hannu saboda an toshe hanyoyi da dama na wawurar dukiyar kasa da suke ba gaira ba dalili!

A gefe daya ga jam’iyyar adawa ta PDP ta sako Baba Buhari a gaba tana zagon kasa a kan dukkan wani kokari da yake na ganin ya cika alkawuran da ya dauka ga ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabensa. 

Ta hada kai da tsinannun ’yan kasuwar da ba sa tausayin talaka, suna ta gana masa azabar da za ta karasa dan sauran tunanin da yake na gyaruwar lamurran kasar nan, da nufin cimma mummunar manufarsu ta son sake dawowa karagar mulki a shekarar dubu biyu da sha tara ko ta halin kaka.

Hakika mun kyautata zato ga dukkanin zababbunmu na APC. Mun yi zaton za su mara wa Baba baya don a fitar da mu daga halin kaka ni-ka-yin da jam’iyyar PDP ta yi sanadiyyar shigarmu a tsawon bakin mulkinta na shekara 16. 

Amma kash! Sai muka ga sabanin hakan. 

Muna fatan 2019 Baba ba zai ba mu umarnin yin SAK ba, don zahiri indai irin wancan tarkacen za a sake kwaso mana to za mu iya cewa SAM!!

 

KABIRU MAIGARI GUMEL. 08028480098./08065642652. 

BIRU MAIGARI [email protected]