Zaben 2019: Babu yarjejeniya a tsakanin APGA da PDP a Nasarawa – Labaran Maku
Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APGA, Labaran Maku ya musanta labarin da jaridar THE EYE WITNESS da ake bugawa a Lafiya fadar Jihar Nasarawa cewa jam’iyyarsa ta APGA ta cimma yarjejeniya da PDP don tunkarar Jam’iyyar APC a jihar a zaben 2019. Mista Labaran Maku wanda shi ne Babban […]

Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APGA, Labaran Maku ya musanta labarin da jaridar THE EYE WITNESS da ake bugawa a Lafiya fadar Jihar Nasarawa cewa jam’iyyarsa ta APGA ta cimma yarjejeniya da PDP don tunkarar Jam’iyyar APC a jihar a zaben 2019.
Mista Labaran Maku wanda shi ne Babban Sakataren APGA na kasa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya ce labarin kanzon kurege ne mara tushi, “Na yi mamaki matuka bayan na karanta labarin da aka buga a jaridar THE EYE WITNESS ranar 28 ga Agustan 2018 cewa ni da jam’iyyarmu mun kammala shirin yin hadaka da PDP a jihar don kau da Jam’iyyar APC a 2019. Ina so in bayyana wa duniya cewa wannan labarin kanzon kurege ne mara tushi kuma mahassada ne suka ingiza aka wallafa don jawo min bakin jini daga wurin dimbim masoyana da Jam’iyyar APGA a jihar da kasa baki daya, kuma da yardar Allah ba za su yi nasara ba,” inji shi.
Mista Maku ya kara da cewa babban manufar wallafa labarin shi ne a kawo masa matsala da kuma durkushe daukakar da a cewarsa ya kawo wa Jam’iyyar APGA a jihar da kasa baki daya tun shekarar 2015 da ya fara yakin neman zaben Gwamnan Jihar Nasarawa. Sai ya bukai al’ummar jihar su yi watsi da labarin kuma su ci gaba da ba jam’iyyar cikakken goyon baya don a cewarsa jam’iyyar ba ta bukatar hada-kai da wata jam’iyyar kafin ta samu nasara a 2019.