Zaben 2019: Buhari ya yi alkawarin inganta rayuwar ‘yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya godewa ‘yan Najeriya bisa karamcin da suka yi masa na sake amince wa da shi don sake tsaya wa takara shugaban kasa karo na biyu a 2019. Buhari ya bayyana hakan ne a babban taron jam’iyyar APC da aka yi Abuja. Shugaban ya kuma bayyana nasarorin da mulkinsa ya samar […]

Zaben 2019: Buhari ya yi alkawarin inganta rayuwar ‘yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya godewa ‘yan Najeriya bisa karamcin da suka yi masa na sake amince wa da shi don sake tsaya wa takara shugaban kasa karo na biyu a 2019.

Buhari ya bayyana hakan ne a babban taron jam’iyyar APC da aka yi Abuja. Shugaban ya kuma bayyana nasarorin da mulkinsa ya samar wa ’yan Najeriya daga shekarar 2015.

Shugaba Buhari ya kara godiya ga ‘yan Najeriya da irin goyon bayan da suka ba shi, don kawo sauyi ga ‘yan kasar.