Zaben 2019: Gwamnan Legas zai fice daga APC?
Ana rade-radin cewa Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode yana cikin tattaunawa da manyan hadimansa domin yanke shawara ta karshe a kan yadda ya dosa ko kuma inda zai dosa a siyasance. A cewar kafar Daily Post, Gwamna Ambode yana shawarar ficewa daga APC din bayan an samu labarin cewa ya samu matsala da uban gidan […]

Ana rade-radin cewa Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode yana cikin tattaunawa da manyan hadimansa domin yanke shawara ta karshe a kan yadda ya dosa ko kuma inda zai dosa a siyasance.
A cewar kafar Daily Post, Gwamna Ambode yana shawarar ficewa daga APC din bayan an samu labarin cewa ya samu matsala da uban gidan siyasar Legas kuma jagorar Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Rade-radin ya nuna cewa Tinubu yanzu ba ya tare da Gwamna Ambode, don haka yake son yam aye gurbinsa a zaben na badi.
Tuni dai aka ruwaito cewa Gwamna Ambode yana shawarar komawa Jam’iyyar PDP ko Jam’iyyar ADC.