Zaben 2019: Hattara dai ’yan Arewa
Wani muhimmin batu da nake so in fadakar da al’umma musamman ’yan yankin Arewa da ke zaune a Kurmi, shi ne wadansu daga cikinmu mun kwashe shekara da shekaru a Kurmi. Kai hasali ma wadansu a nan suka hayayyafa, suka yi ’ya’ya da jikoki inda ya zama tamkar garuruwanmu na asali. Sai dai akwai wani […]
Wani muhimmin batu da nake so in fadakar da al’umma musamman ’yan yankin Arewa da ke zaune a Kurmi, shi ne wadansu daga cikinmu mun kwashe shekara da shekaru a Kurmi. Kai hasali ma wadansu a nan suka hayayyafa, suka yi ’ya’ya da jikoki inda ya zama tamkar garuruwanmu na asali. Sai dai akwai wani karin magana da Hausawa kan ce ne kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka duk lokacin da za mu gudanar da harkokinmu, mu rika tunawa da asalin inda muka fito, wato mu al’ummar yankin Arewa. Mu sani, ko ba jima, ko ba dade za mu koma gida.
Nasihar da zan yi mana ita ce, ga shi zaben 2019 ya karato inda tuni ma har an fara kamfe. Don haka yana da kyau al’umma Musulmi da Kirista musamman na Arewa da na kasa baki daya mu yi nazari a kan irin shugabannin da suka kamata mu zaba. Don yanzu kan mage ya waye, an sha mu, mun kuma warke musamman a kan irin zaben da muka yi a 2015 inda muka turo mota amma ta tafi ta bade mu da kura.
Alal hakika mu dage wajen zaben shugabannin nagari, masu kishinmu, ba masu kin mu ba. Wadanda za su share mana hawaye, su kare mana hakki, su tsare mana mutuncinmu da na addininmu, ba masu son tara abin duniya don kece-raini da nuna isa ba.
Sannan mu yi la’akari da ’yan kungiyar asiri masu shanye jinin mutane don biyan bukatunsu, ba biya wa talakawan kasa bukata ba.
Sannan mu yi hankali da lalatattu ’yan luwadi da masu yin madigo da masu neman matan banza da ’yan sharholiya. Kada mu kuskura mu zabi irin wadannan mutane a matsayin shugabanni a kowane mataki.
Sannan ina kira ga Musulmi da Kirista musamman na yankin Arewa mu sani babu addinin da ya yarda mu zabi batagari masu wawure dukiyar kasa. Sannan mu zauna da junanmu lafiya don a samu ci gaban kasa.
Mu tuna yankin Arewa ne ya fi samun koma-baya a dukan yankunan da muke da su a kasar nan. Yanzu da Allah Ya kawo mana Shugaba Muhammadu Buhari mai gaskiya da rikon amana, ya kamata mu mara masa baya a zabe mai zuwa, don ci gaba da samar mana da abubuwan more rayuwa.
Kada mu yarda da mayaudara, masu bayar da kudi don a zabe su. Idan kuwa suka ba mu kudi, to mu karba mu biya bukatarmu, sannan a ranar zabe sai mu zabi abin da ya dace.
Ina ganin idan muka yi haka, ko shakka babu masu niyyar amfani da kudi don a zabe su, za su shiga taitayinsu, don sun san ko sun bayar da kudin ba za su yi wani tasiri a kan talakawa ba.
Sannan ina kira mu zauna da juna lafiya, domin tashin hankali ba zai haifar mana da komai ba, sai koma baya.
In mun lura duk lokacin da aka samu wani tashin hankali, irin batagarin shugabannin da ke rura wutar rikicin za ka tarar sun kwashe matansu da ’ya’yansu sun bar kasar zuwa wata kasa daban don su huta. Sun bar talakawa ana kashe kansu, ba ruwansu, kuma babu wani taimako da za su yi musu.
Mu lura duk kasar da take rikici, babu wani ci gaba da take samu, sai koma baya.
Don haka ina kira ga ’yan Arewa musamman mazauna Kudu mu yi kokarin komawa gida don mu yi zabe. Kada mu ce ba ruwanmu da zabe, don ta hanyar zabe ne za ka iya zaben shugaba nagari, a yankinka da garinku da jiharku da kuma Najeriya.
Ina yi wa ’yan Arewa mazauna Kudu nasiha mu rika komawa gida don ziyartar iyali. Ba daidai ba ne ka ga wani dan Arewa ya shafe shekara da shekaru yana zaune a Kurmi amma ya manta da danginsa da abokansa da sauran ’yan uwa. Gaskiya yin haka ba daidai ba ne.
Ina rokon Allah Ya kai mu zaben 2019 lafiya, kuma Ya ba mu ikon zaben shugabanni nagari. Allah Ya sa a yi zaben lafiya. Kuma Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya Ya ba mu karuwar arziki mai yawa.
Abdullahi Husaini ya rubuto ne daga Lamba 83 Ikwerre Road Fatakwal 08036899117