Zaben 2019: Jihohin Arewa sun dauki harama

A daidai lokacin da ake gab da buga gangar siyasar yakin neman zabe na jihohin kasar nan, wakilanmu a wasu jihohin Arewa sun yi nazari tare da duba mana yadda tukwanen siyasar suka fara tafasa, inda wasu gwamnoni ke shirin sauka su mara baya ga magadansu, yayin da wasu kuma ke hankoron sake komawa wa’adi […]

Zaben 2019: Jihohin Arewa sun dauki harama

A daidai lokacin da ake gab da buga gangar siyasar yakin neman zabe na jihohin kasar nan, wakilanmu a wasu jihohin Arewa sun yi nazari tare da duba mana yadda tukwanen siyasar suka fara tafasa, inda wasu gwamnoni ke shirin sauka su mara baya ga magadansu, yayin da wasu kuma ke hankoron sake komawa wa’adi na biyu. Duk da cewa karawar ta 2019 za ta fi zafi ne tsakanin Jam’iyyun APC da PDP musamman a Arewa, idan ka dauke jihohin Bauchi da Kano da kuma Kaduna, za ka iya cewa ragowar jihohin Arewar duk manyan Jam’iyyun APC da PDP ne za su fafata. Ga yadda nazari da hasashen suka kasance:

Jihar Kaduna

Akalla ’yan takara 36 ne ke neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyu 36 sai dai an fi ganin takarar za a yi ta ne a tsakanin Gwamna mai ci a yanzu Malam Nasir El’rufai na APC da kuma Isa Ashiru Kudan na PDP.

Alamu na nuna cewa komai na iya faruwa a zaben mai zuwa, domin jam’iyyun nan biyu kowannensu na hangen nasara a tattare da shi. ýA misali, PDP na ganin matakan da Gwamnatin APC a jihar ta dauka wajen korar ma’aikatan kananan hukumomi da malaman Makaranta da masu unguwanni da kuma rusa gidajen talakawa da ke a Zariya da kuma rusa wasu shaguna a cikin garin Kaduna za su taimaka wa dan takararta wajen lashe zaben.

Su kuma jam’iyar APC a nasu ganin, har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da sauran farin jini wajen talakawa. Don haka suna ganin za su fake da wannan farin jini nasa wajen cin zabe. Baya ga wannan kuma shi gwamnan jihar yana ganin dukkan matakan da ya dauka ya yi hakan ne domin inganta rayuwar talakawan jihar. Sannan kuma ya dauki mace Musulma daga Kudancin jihar, abin da ba a taba yi ba a jihar, wanda masana ke ganin ya yi hakan ne domin samun goyon bayan Musulmi, duk kuwa da cewa shi ya ce bai dauke ta saboda Musulunci ba sai domin cancanta.

Jihar Kano

A yanzu haka dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kafe jerin sunayen mutanen 54 masu zawarcin kujerar Gwamnan Jihar Kano, inda alamu ke nuni da cewa kujerar ka iya zama ta mai rabo. Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa jam’iyyu uku ne suka yi wa sauran fintinkau wajen tallata manufofinsu da ’yan takararsu wandak uma ake sa rai Gwamnan jihar na gaba zai fito daga cikin wadannan jam’iyyu.

Idan muka dauki Jam’iyyar APC wacce Gwamnan Jihar mai ci yanzu DoktaAbdullahi Umar Ganduje ke yi wa takara, akwai ’yan rigingimu a ciki da hakan ka iya zama barazana ga jam’iyyar. Rigingimu da suka hada da rikicin cikin gida, sakamakon wasu da suke ganin an bata musu ta hanyar kin ba su takarar mukaman da suka nema, wanda ake ganin za su yi zagon kasa wato su zabi wata jam’iyya daban. A gefe guda kuma ga bayyanar faifan bidiyon da ake zargin Gwamnan da karbar na goro daga hannun ’yan kwangila. Kodayake Gwamnatin ta sha fitowa tana bayyana cewa duba da irin wanan tirka-tirkar da ke faruwa a jam’iyyar, hakan bai yi wani taisirn a-zo-a-gani a kan karbuwar jam’iyyar ba, domin a cewarsu ’yan dangwale za su zazzage wa jam’iyyar ta APC a kuri’unsu.

Idan muka dauki Jam’iyyar PDP, wacce Abba Kabiru Yusuf wanda ya fito daga PDP tsagin Kwankwasiyya ke yi wa takara, za mu ga cewa akwai kalubale a ciki, duba da yadda ake kai kawo a kan harkar takarar, lamarin da ya fusata sauran ’ya’yan jam’iyyar har suka fice daga jam’iyyar ganin cewa ba a yi musu adalci.

Jam’iyya ta uku da ke da muradin kwace kujerar Gwamnan, ita ce Jam’iyyar PRP, wacce ake ganinta a matsayin mafakar fusatattun ’ya’yan jam’iyyu daban-daban. Dan takarar jam’iyyar mai suna Salihu Sagir Takai, wanda shi ma fusatacce ne daga Jam’iyyar PDP. Sai dai duk da ganin da ake yi wa jam’iyyar ta PRP a matsayin sabuwar jam’iyya amma a bayyana yake yadda al’umma ke tururuwar komawa jam’iyyar a kullum. Don haka jam’iyyar ta PRP na iya lashe kujeru daban-daban a Jihar Kano.

Jihar Sakkwato

Da wahalar gaske jam’iyar PDP za ta samu nasara kan APC a zaben nan na 2019 a Jihar Sakkwato, ganin yanda lamurra ke tafiya a sha’anin jam’iya da gwamnati wadda mafi yawan jama’ar jihar ke kallon tana tafiyar hawainiya, wadda ta kasa kai bantenta, inda kowa ke yin tasa rawar gani ba tare da an yaba ba.

Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, raba garin da ya yi da Gwamna Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya canja yanayin siyasar Sakkwato. Zaben 2019 jayayya ce tsakanin Gwamna Tambuwal wanda yake tare da tsohon Gwama Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa da sanannen dan siyasar nan Alhaji Umarun Kwabo A.A. a jam’iyar PDP, da bangaren Sanata Aliyu Wamakko shi kadai tare da yaransa a APC.

Jihar Katsina

Babban ƙalubalen da ke fuskantar manyan jam’iyyu biyu da ke da ƙarfi a Jihar Katsina, APC mai mulki da kuma PDP mai adawa shi ne, yaƙin cikin gida. A APC, Gwamna Masari wanda jama’a ke kallonsa da ƙima matuƙa, wanda aka shaida kirkinsa a matsayin shi kansa amma hakan bai hana shi fuskantar ƙalubalen riginginmun siyasarsa ta cikin gida ba.

Baya ga ƙungiyar APC Aƙida wadda ke adawa da Gwamnatin ta Masari a cikin gida, wani abin da ke nuni da wata barazana ce ga sake zabensa na 2019 shi ne irin ƙorafe-ƙorafen da wasu ’yan’yan jam’iyyar ke yi, musamman a zaɓen fidda gwani na ’yan takara da ya shuɗe, wadanda suka haɗa har da kujerar Gwamna.

A nata ɓangaren, jam’iyar adawa ta PDP da ke jihar, tuni da ma ta saba fuskantar irin waɗannan matsaloli na cikin gida. To sai dai a wannan karon abin ya janyo mata koma baya matuƙa wanda har ya sa ta rasa wasu jiga-jigan jam’iyar waɗanda suka yi canjin sheƙa zuwa jam’iyar APC. Cikinsu har da Umar Tsauri, wanda aka fi sani da lakanin Tata, wanda ya fice daga PDP ya koma APC; mutumin da a baya har kotu sun zauna bisa zarginsa da ƙoƙarin tayar da fitina a ƙarƙashin wani shiri da ya ɓullo da shi mai taken “A Kori Yunwa.”

Jihar Nasarawa

Kalubale da dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APC, Abdullahi Sule ka iya fuskanta bai tsaya ga zabin dan takarar Gwamna na PDP a jihar, Dabid Ombugadu ba, babban kalubalen shi ne dan takarar gwamna na Jam’iyyar APGA, Mista Labaran Maku.

Wani daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a jihar da ya bukaci a sakaya sunansa ya  shaida wa wakilinmu cewa shugabancin jam’iyyar a jihar tuni ya gano wani shiri na musamman da wasu al’ummar Kiristoci ’yan kabilar Alago da Eggon, wadanda su ne manyan kkabilu da suka fi yawa a jihar ke yi na cewa za su fito kwansu da kwarkwata domin su zabi tsohon Ministan Labarai na Jam’iyyar APGA, Mista Labaran Maku.

Yanzu da Maku na APGA da Ombugadu na PDP, kasancewa dukkansu Kiristoci ne suna gasar neman goyon bayan Kiristocin jihar ne kuma wakilinmu ya gano cewa galibin Kiristocin jihar suna tare da Maku ne a zaben 2019. Sai dai wata majiya a APC ya shaida wa wakilinmu cewa duk da wannan taron dangi da ake yi wa dan takarar Gwamna a APC, jam’iyyar za ta kada dukan sauran ’yan takarar ta lashe zaben na 2019.

Jihar Gombe

A zaben da ke tafe na shekarar 2019 a Jihar Gombe, akwai manyan ’yan takara biyu a jam’iyyun APC da PDP, wato Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a APC da Sanata Usman Bayero Nafada a PDP, a yayin da Gwamna Ibrahim Hasasan Dankwambo ke barin gado don neman Sanata daga Gombe ta Arewa a Jam’iyyar PDP. Don haka takarar za ta yi zafi ne tsakanin masu nema da ke kasa, duk da cewa wasu na ganin PDP za ta iya samun nasara, kasancewar ita ce ke kan karaga, amma kuma wasu na ganin cewa ba a nan gizo ke sakar ba. Saboda a cewarsu, al’umma ta fara gajiya da mulkin PDP, wacce ta ke kan mulkin jihar tun 2003.

Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya na APC attajiri ne kuma tsohon Kwamishinan Kudi a jihar, wanda ake ganin farin jininsa ya sake farfadowa idan aka yi la’akari da can baya, inda ya gaza tabuka abin a zo a gani, duk kuwa da irin guguwar sauyi ta APC da ta kada a Arewa, amma bai kai labari ba.

Daga cikin abubuwan da suka kara wa tafiyarsa karfi akwai goyon baya da ya samu daga dukkan manyan ’yan siyasar APC wadanda ya kada su a zaben fidda gwani. Haka kuma mutum ne da ake gani natsattse, wanda ba ya sa kansa cikin duk wani shashanci ko rashin mutunci kuma bai da wata matsala irin ta goya wa ta’addanci irin na ’yan Kalare baya.

Jihar Filato

A  Filato, Jam’iyyar APC ta sake tsayar da Gwamna Simon Lalong ne, a yayin da Jam’iyyar PDP da ta tsayar da tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu, Janar Jeremia rUseni mai ritaya. Shi dai Gwamna Lalong ya fito ne daga Karamar Hukumar Shendam da ke yankin Kudancin Jiha, a yayin da shi ma Sanata Jeremiah Useni, ya fito daga Karamar Hukumar Langtang da ke Kudancin Jihar.

Dukkan bangarorin wadannan ’yan takara kowannensu yana ikirarin cewa shi ne zai lashe wannan zabe. To amma an yi hasashen cewa bisa la’akari da yanayin yadda siyasar jihar take tafiya yanzu, da kuma yadda ’yan takarar suke a idanun al’ummar jihar; zai yi wuya Jeremiah Useni ya iya kawar da Gwamna Lalong daga kan wannan kujera.

Har’ila yau masu lura da harkokin siyasar sun yi bayanin cewa ganin irin kokarin da Gwamna Lalong ya yi, wajen samar da zaman lafiya a Jihar da warware matsalar biyan albashin ma’aikata, tare da tafiya da kowa a gwamnatinsa, ta hanyar raba mukamai ga al’ummomin jihar da tallafa wa harkokin noma, zai yi wuya a iya kayar da shi a zaben. An nuna cewa zai iya lashe kananan hukumomi 15 cikin 17 da ke jihar.

Masu lura da al’amuran siyasar sun bayanin cewa babu shakka akwai matsaloli masu yawa da za su iya kawo wa Janar Jeremiah Useni tarnaki wajen kawar da Gwamnan Lalong daga kan kujerar gwamnan jihar ta Filato. Suka ce kamar a zaben shekara ta 2015, PDP ta yi babban tasiri a yankin Filato ta Arewa, musamman a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Riyom da Barikin Ladi. Amma ganin yadda wani jigo a jam’iyyar ta PDP kuma dan Majalisar Wakilai ta Tarayya Edward Pwajok ya fice daga jam’iyyar, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa tun a shekara ta 2017. Don haka suke ganin jam’iyyar za ta iya samun matsala a yankin.

Wata babbar matsalar kuma ita ce wasu jiga -jigan jam’iyyar, basu ji dadin tsayar da shi ba, musamman tsohon gwamnan Jihar Jonah Jang, donhaka ana ganin babu alaka mai kyau tsakaninsu.

Hasashe ya nuna cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar da ba su ji dadin tsayar da Jeremiah Useni ba, don haka za su iya ficewa daga jam’iyyar kafin lokacin zaben, su dawo jam’iyyarAPC. An ce da wuya dan takarar na PDP ya iya lashe kananan hukumomin da suka wuce Langtang ta Arewa da Langtang ta Kudu, cikin kananan hukumomin Jihar 17. Don haka suke ganin zai yi wuya Useni ya iya kawar da Lalong daga kujerar Gwamnan Filato a wannan zabe na shekara ta 2019.

Koma dai yaya ta kaya, kallo ya koma 2019 idan Allah Ya kai mu, inda mai rabo ne kadai ka iya cin ma nasara.