Zaben 2019: Ku zabi mai gaskiya da rikon amana – Sheikh Jingir
Ku yi aiki da hankalinku ku zabi abin da zai fisshe ku – Sheikh Dahiru Bauchi Abin da ya kamata ku yi la’akari da shi – Dokta Gumi Kasancewar manyan ’yan takarar Shugaban Kasa biyu Shugaba Buhari da Atiku Abubakar, sun fito daga addini daya da yankin daya ya takaita zafin siyasa da za a […]
Sheikh Sani Yahya Jingir
Sheikh Xahiru Usman Bauchi and
Dokta Ahmad Gumi
Ku yi aiki da hankalinku ku zabi abin da zai fisshe ku – Sheikh Dahiru Bauchi
Abin da ya kamata ku yi la’akari da shi – Dokta Gumi
Kasancewar manyan ’yan takarar Shugaban Kasa biyu Shugaba Buhari da Atiku Abubakar, sun fito daga addini daya da yankin daya ya takaita zafin siyasa da za a iya fuskanta a zabe mai zuwa. Wannan ya sa lokacin da Aminiya ta tuntubi wadansu daga cikin manyan malaman kasar nan da suka hada da Shugaban Izala Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir da Sheikh Dahiru Bauchi da Dokta Ahmad Gumi suka nuna cewa akwai alamun zaben zai gudana cikin kwanciyar hankali. Sai dai sun bayyana abubuwan da suka kamata mutane su lura da zu a yayin zaben kamar haka:.
A zaben Shugaban Kasa na badi Musulmi biyu ne manyan ’yan takara. A matsayinku na shugabannin Musulmi me ya kamata su lura wajen zaben wanda zai shugabancin kasar a zabe mai zuwa?
To, ni zan yi magana ce a mahangar Musulunci, a tsarin Musulunci siyasa da jagoranci babu wanda aka cire wa, nauyi ne da ya rataya a kan kowa. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce Shugaban Kasa a matsayinsa na shugaba, makiyayi ne na al’ummar kasar da yake yi wa shugabanci. Yana kiwon rayuwar mutanen kasar da dukiyarsu da tattalin arzikinsu da lafiyarsu da ci gabansu da dukan abubuwan da dan Adam yake bukata.
Har ila ya ce magidanci makiyayi ne ga mutanen gidansa. Ka ga gwamnati tun daga gidajen jama’a take tasowa ke nan. Don haka a Musulunci dukanmu makiyaya ne. Saboda haka maganar za a yi zabe a Najeriya a tsarin Musulunci, babu wani abu da ba za a yi shi lami lafiya ba. A nan abin da zan yi magana shi ne, dukanmu Musulminmu da Kiristocinmu da wadanda ma ba su da addini, kowa ya yi niyyar zabar wanda zai gina kasar nan saboda Allah.
Mu lura da mai imani, domin dan duniya babu ruwansa da imani da tunanin cewa za a tsayar da shi a gaban Allah, a ranar tashin Alkiyama. Komai aka ba shi zai cinye, babu ruwansa da maganar tashin Alkiyama. Don haka dole ne mu samu wane ne mai imani da mika wuya ga dokokin Ubangiji. Saboda haka idan wannan zabe ya zo, cikin wadannan ’yan takara, mu zabi mai imani da addini da gaskiya da rikon amana da cika alkawari. Mu kiyayi kwadayi, duk wanda ya ce ga ransa na sayarwa ne, a ba shi kudi, wannan mutum masifa ne a kansa, masifa ne a kasar, masifa ne ga wanda ya zaba da wanda ba ya so. Don haka mu kiyayi duk abin da ba ya da kyau, kada kwadayin kudi ko mulki ya batar da hankalinmu.
Sannan wadanda suka fito takara su sani, akwai tambaya a kansu a duniya da Lahira. Kuma kada mu dube su ta hanyar wurin zamansu ko kabilarsu ko addininsu, mu dube su ta hanyar aiki mai kyau. Kuma mu yi addu’a Allah Ya zaba mana mai kyau domin kasarmu ta yi kyau, mu rika noma abincin da za mu ci, mu iya yin sana’o’i a gina mana masana’antu.
Kuma duk wanda muka samu ya taba kulla wa Najeriya sharri kada mu zabe shi. Duk wanda ya damu da kasar nan mu zabe shi. Saboda haka ni ba ni da wani mutum da na sani, sai dai ina rokon Allah Ya dora ni a kan mai kyau.
Sace-sacen mutane da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa, wadansu mutane na ganin kamar sha’anin tsaro ya dogara ne ga gwamnati. A musulunce sha’anin tsaro ya dogara a kan wane ne?
Maganar tsaro ta shafi al’umma ce baki daya. Babu wanda aka ware amma akwai wadanda suka fi karfi, wadanda suka fi karfin nan kuwa gwamnati ce kan gaba. Babu wanda ya kai gwamnati karfi kan maganar tsaro, idan gwamnati ta samu rauni kan tsaro to kowa ya samu rauni. Babban abin da ya kamata gwamnati ta yi kan tsaro shi ne ta samar wa mutane aiki, ta biya ma’aikatan gwamnati hakkokinsu da za su iya rayuwa. Kuma ta bude wa manoma hanyoyin bunkasa noma da hanyoyin da za su rika sayar da kayayyakin amfanin gonarsu ba tare da sun wahala ba. Idan mutum ya samu aikin yi, ya samu abinci, ka ce ya koma daji ya rika arangama da macizai da sauran namun daji, yana satar mutane ba ta taso ba.
Na biyu, tun daga gidajen iyaye su dubi irin tarbiyyar ’ya’yansu, su koya musu sana’o’i, su koya masu noma da kiwo. Idan iyaye suna yi wa ’ya’yansu tarbiyya tagari, zai yi wuya a samu wanda zai tafi daji yana sace-sacen mutane. Ka ga a nan iyaye suna da gudunmawar da za su bayar wajen harkokin tsaro a kasar nan.
Ku yi aiki da hankalinku ku zabi abin da zai fisshe ku – Sheikh Dahiru Bauchi
Musulmi biyu daga Arewa ne manyan ’yan takara a zaben Shugaban Kasa na 2019, wane kira za ka yi ga al’umma game da zabe mai zuwa?
Ina ba da shawara ga mutanen Arewa da sauran al’ummar Musulmi cewa kowa ya zabi abin da ya fi amince masa, abin da duk hankalinka ya kama cewa zai biya maka bukatunka da kai da ’yan uwanka, ka zabe shi Allah kuma in Ya taimaka Ya zaba masa abokan aiki nagari, don bukatar ta biya. Asalin siyasa abin da ake kira siyasa wani abu ne da talakawan kasa suke nema ba su samu ba, kudi ba zai iya kawo musu abin ba, gayya ba zai ta kawo abin ba, sai gwamnati. Wani abu suke tsoro wanda ko yana tare da su a yanzu ko kuma zai zo nan gaba, ba kuma abin da zai raba su da wannan abin da suke jin tsoro, ko kudi ko gayya sai dai gwamnati. To sai a samu wadansu maza su yi damara, su zo su tsaya a gaban mutane su ce ya jama’a, abin da kuke nema ba ku samu ba saboda matsayinku na ’yan kasa da kudi ko gayya ba za su iya kawo muku ba sai gwamnati, in kuka zabe ni na zama gwamnati wallahi abin zan kawo muku shi. Ya yi rantsuwa, ya ci gaba da cewa kuma abin da kuke tsoro wanda kudi ko gayya ba za su iya kare muku shi ba sai gwamnati, in kun zabe ni zan kawar muku da wannan abin da ba ku so din. To, sai a yarda da rantsuwarsa da alkawarinsa a zabe shi.
In an zabe shi, a ba shi dama ya yi shekara hudu kamar yadda muke yi a Najeriya ko shekara biyar ko bakwai, kamar yadda ake yi a wasu wurare. To, a cikin shekarun da zai yi sai a duba a ga alherin da ya yi alkawari zai kawo wa jama’a, wanda ba za su iya kawo wa kansu ba in ya zama gwamnati, shin ya kawo musu? Ko sharrin da ya yi rantsuwa, ya yi alkawarin zai tunkude wa jama’a in ya zama gwamnati kuma ga shi ya zama gwamnati ya tunkude musu?
To, in ya jawo alherin da ya yi alkawari kuma ya ture sharrin da ya yi alkawari, ya yi daidai, sai a sake zabensa in ya sake tsayawa. In kuwa bai kawo alherin ba kuma bai tunkude sharrin ba, to alkawari bai cika ba saboda haka abin da ake lura ke nan kuma kowa yana da hankalinsa, ya san alherin kuma ya san sharrin. In an kawo alheri ya sani, in an ture sharri ya sani, don haka a bar mutane da hankalinsu su zabi abin da suke gani shi ne zai fisshe su.
Wadanne abubuwa ya kamata jama’a su lura da su wajen zaben Shugaban Kasa da sauran mutanen da za su mulki Najeriya a matakin tarayya da jihohi?
To, abin namu yana da kamar wahala, tunda duk wanda ka zaba ba shi kadai zai yi mulki ba, dole akwai mutane tare da shi kuma akwai mutane a karkashinsa. Ka ga gwamnatin da muke ciki ta yanzu ba sosai muke jin dadinta ba, amma kuma abin ba daga shugabanta ba ne, wanda aka zaba. Abin daga wadanda suke tare da shi ne muke samun damuwa. Damuwar ma wasu ba za mu iya fada ba, saboda idan mutum ya fadi wani abu da ya shafi sukar wannan gwamnati ko shugabanta, kamar ya soki kansa ne in mutumin Arewa ne Musulmi. To amma akwai wasu abubuwa da ba su da dadi amma an ce wadansu ne da suke tare da shi su suke haddasawa. Saboda haka in an zabi mutumin kirkin sai a taya shi mu yi ta rokon Allah, Allah Ya ba shi shi ma mutanen kirkin da za su taimaka masa. Abin da za mu yi ke nan, in an ga mutumin kirki ne aka zabe shi to shi ma Allah Ya ba shi mutanen kirki da za su taimaka masa, ko don a samu sauki.
Har yanzu ana fama da matsalar tsaro da sace-sacen mutane, me Shehi zai ce?
Wallahi abin da yake faruwa a yanzu na kashe-kashen mutane, musamman abin da ya faru a Jihar Taraba da abin da yake
faruwa a Zamfara da wasu wurare na kashe-kashe da sace mutane da ke faruwa a Kaduna da wasu wurare, abin ba ya da kyau ko kadan. Saboda haka abin bai da magani sai addu’a. Ita gwamnati da ma garkuwarta sojoji, to sojojin ma an soma kashe su, inda aka kashe sojoji fiye da dari. To ka ga an yi wa kasa rotsi, an karya mata babbar garkuwarta. Don su soja su ne garkuwar kasa, ban da addu’a ba abin da yake maganin wannan kuma addu’ar da za a yawaita ita ce ‘Hasbunallahu wa ni’imal wakilu.’ A yi sau 450, wanda ya samu dama ya rika yin 1,350.
Kuma babban abin da ya jawo wadannan fitinu duka shi ne fada da aka yi da Allah. Allah Ya ce duk wanda ya cuci waliyyina, ya zalunce shi to na sanar da shi zan yi yaki da shi. To akwai wadansu mutane a Najeriya, ban da zagin waliyyai da kafirta Musulmi, ba abin da suka sa a gaba. Sai su kafa makaranta, su jawo ’ya’yan mutane su sa a ciki, su yi ta zagin waliyyai, su koya musu zagin waliyyai, su koya musu kafirta Musulmi, ba abin da za a jawo wanda zai amfani Musulunci ba ne suke yi, sai dai wanda zai watsa Musulunci.
To, in an ce Musulunci, waliyyai babu su dodanni ne, Musulmi masu Sallah ba Musulmi ba ne kafirai ne, to ina Musuluncin yake? Ka ga an rushe Musuluncin gaba daya. To, irin wadannan su suka jawo Allah Ya yi fushi, Yake dukanmu da bindigogi, Yake dukanmu da bama-bamai, Yake dukanmu da bala’o’i iri-iri saboda fushin da Ya yi, an zagi waliyyanSa, an yi gaba da su kuma ana ci gaba da koyar da jahilai zagin waliyyan Allah da kafirta Musulmi.
Wadansu har matan Annabi (SAW) zagi suke yi, wadansu har sahabban Annabi zagi suke yi, kuma muna tare da su a kasar nan. Ai ko Amurka ce ta ce za ta yaki wadansu mutane a wannan kasa mun kade, balle Allah Ya ce zai yaki wadansu mutane kuma mutanen muna tare da su a kasa daya, a jiha daya, a gari daya, wani wurin unguwa daya har gida daya. Ina zama lafiya an zama madakin gobara? Ya kamata masu zagin waliyyai da kafirta Musulmi da masu zagin sahabbai da masu zagin matan Manzon Allah (SAW) su janye zagin da suke yi, in suna so mu zauna lafiya.
Abin da ya kamata jama’a su yi la’akari da shi – Dokta Gumi
Da farko wannan zabe na shekarar 2019, muna fata a yi shi cikin lafiya a kuma kare shi lafiya, domin yana da wuya wani ya labe da bangaranci ko ya labe da addini ko ya labe da wani dalili ya kawo rikici. Tunda dai kamar yadda ka ce, dukansu ’yan yanki daya ne kuma addini daya suke.
Saboda haka muna fatan zaben zai bai wa wannan kasa ’yanci kuma zai bai wa mutane damar zaben wanda suke so. Kuma kowa a bar shi ya zabi wanda ya yi masa daidai.
Wadanne abubuwa ya kamata a lura da su yayin zaben wadanda za su mulki kasar nan a matakin tarayya da jihohi?
Kamar mu dai Musulmi kuma addininmu ya yi mana tattalin abubuwan da ya kamata mu duba, domin shugabanci amana ne kamar aure. Annabi (SAW) ya ce wanda duk ya zo muku kuka yarda da addininsa da halayensa, ya nemi ’yarku, ku ba shi. In ba ku yin haka kuwa fitina da fasadi za su watsu a cikin kasa.
Wato idan mutum ya zo dole a duba halayensa. A bangaren aure ke nan, balle kuma mulkin kasa. Mulkin kasa dole sai an duba an kuma yi la’akari da abubuwa da yawa. Farko dai abin da ake so shi ne jama’a su zabi shugaban da suke so, wanda ke da halaye na shugabanci, halayen shugabancin kuwa su ne hada kan al’umma.
Wanda zai iya janyo wannan da wancan a hada kai domin a tafi tare kuma ana son mai tausayi da afuwa kamar yadda Allah Ya ce. Ana kuma son mai gaskiya, mai amana, mai rashin yaudarar mutane, mai kuma kwatantawa. Idan an samu wadannan duka a wajen mutum, shi ya fi cancanta a bai wa mulki. Amma a yanzu kasantuwar zamani ya yi nisa, za ka samu wasu bangaren suffofin a wajen wani wasu kuma a wani. Shi ya sa kamar yadda yake a cikin wani littafin Imam Ibn Tirmiyya mai suna ‘Siyasatul Shar’iyyah’ aka yi tambaya cewa idan ga mutum biyu wani mai karfi amma fajiri, wannan kuma mai rauni amma amini. Wanne ne za a dauka idan an zo ba da kwamanda. Sai Imam Ahmad bn Hambal ya ce, mai rauni amini, rauninsa a kan al’umma yake gaskiyarsa kuma a kansa yake. Mai karfi fajiri, fajircinsa a kansa yake amma karfinsa a kan al’umma yake, wato al’umma su samu shugaba mai iya rike mutane domin ya tunkari al’amura. Saboda haka idan an samu bambance-bambance, abin da ake so mafi a’ala kuma shi ne ya zama mai karfi da zai iya rike al’umma.
Har yanzu ana fama da matsalar tsaro da sace-sacen mutane me, me za ka ce?
To, abin da ya kawo sace-sacen mutane ba wani abu ba ne illa talauci da ya zo wa kasar nan. Duk da cewa kasar nan na da dimbin arziki, abin da kuma ya kawo talaucin nan shi ne fadace-fadace. Masu man fetur sun datse, masu kudi sun janye kudinsu, masu aiko da kudi kowa ya janye domin yana cikin firgita saboda haka kudi bai zuwa.
Ita kuma gwamnati ta rasa kudin da za ta iya rike sojoji da ’yan sanda. Misali, kwanan nan aka kashe sojoji wajen dari. Sun fada cewa tsofaffin makamai ne ke damunsu, wani sojan ma ya ce makaman tun lokacin Shagari aka saye su. To, rashin kudi, yanzu dai ba za a yi tuhuma ba kamar yadda muka yi a wancan lokaci. Mun tuhumi shugabannin baya, ni kaina na tuhume su cewa da gangan suke yi, abin ya zo ya nuna cewa ashe ba da gangan ba ne. Rashin kashe kudi kuma ba a kashe kudin nan da rashin kudi.
Ashe ke nan kun ga duk yanayin da zai kawo rashin tattalin arziki kasa dole a kiyaye, saboda haka mu duba mu gani me zai kawo mana tattalin arzikin kasa, inda kowa zai samu yalwa, soja da ’yan sanda su samu kayan aiki, a kuma kara karfafa su? Idan an samu wannan insha Allah za a samu saukin sace-sacen mutane da ake yi, domin talauci ne ya yi wa mutane yawa.
Kuma ina jan hankali cewa, duk wanda ya samu mulki saura su bi shi, su goya masa baya, babu wata maganar cewa wane ne ya ci. Kuma duk wanda ya ci mulki, ina yi masa wasiyya ya rungumi kowa, har da wadanda suke masa adawa. Ya rungume su domin aikin da ke a gabanmu ya fi karfin mutum daya, ya fi karfin jam’iyya daya. Sai dukan ’yan Najeriya mun hada kanmu za mu iya fita daga cikin masifar da muke ciki.