Zaben 2019: kuri’arka wukarka, in ji dahiru Bauchi

Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya shawarci al’ummar Musulmi da su dauki kuri’arsu a matsayin wukar su ta yanka, wajen maida hankali da kuria’rsu a zabe mai zuwa domin zabar mutanen kirki kan mukamai daban-daban da  za a yi. dahiru Bauchi ya yi wannan kalami ne lokacin da yake jawabi ga […]

Zaben 2019: kuri’arka wukarka, in ji dahiru Bauchi

Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya shawarci al’ummar Musulmi da su dauki kuri’arsu a matsayin wukar su ta yanka, wajen maida hankali da kuria’rsu a zabe mai zuwa domin zabar mutanen kirki kan mukamai daban-daban da  za a yi.

dahiru Bauchi ya yi wannan kalami ne lokacin da yake jawabi ga Alummar Musulmi a taron Maulidin Annabi Muhammadu (SAW) da aka yi a Bauchi, Ya ce “ka dauki kuri’arka wukarka na yanka ko ba wanda zai yanka wuyanka, kuri’arka ko kuma ka ba wanda zai yanka maka, saboda idan ‘yan siyasa suka guje mu, suka ce ba sa sonmu, tun bayan zabe ba zamu sake ganinsu ba, sai lokacin zabe ya karato su lallabo su zo wajenmu neman kuri’a, to muce musu mun gane wayon,  mun hanaka kuri’armu tunda ba ka sonmu, ku ma ba gaba, kuri’a ta ce ba zan baka ba, kamar karatun Sardauna Wal-bani, Wal-baka Wal-hanani Wal-kememe. Mu hada kai baki daya mu zabi masoyanmu wadanda zasu kula mana da mutuncinmu da addininmu kuma wadanda zasu yi mana ayyuka nagari su yi mana adalci”

Shehun Malamin wanda shi ne jagoran darikar Tijjaniyya ya roki al’ummar musulmi da su hada kai da juna su bi umurnin Allah da ManzonSa, ya ce babban abin da ya kawo rarrabuwa a tsakanin al’umma shi ne yadda wadansu mutane suka dauki maganar malamansu cewa shi ne kawai magana, ba su ma yarda da cewa Malaman na iya yin kuskure ba, a ganinsu duk wanda ya sabawa malaminsu ya zama kafiri, sun nada malamansu a matsayin su ne kawai ke da ikon su ce wane musulmi ne kuma wane ba musulmi ba ne, duk wanda ya ki bin abinda suka ce kuma su ce masa kafiri.

Da ya juya kan batun yake-yake da kuma fashi da makami da satar mutane da yin garkuwa da sauran miyagun laifuka kuwa, Shehin malamin ya ce an tsokani Allah ne ta hanyar zagin zababbun bayinsa shi yasa wannan bala’i duka yake samun mu. Sai ya roki Allah Ya kawar mana da fitina ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa Musulunci ya yi umurni ayi jihadi, amma ya bada sharudda da cewa sai musulmi sun cika ka’idojin da musulunci ya shimfida kafin jihadi yake wajaba akansu. Daga cikin ka’idojin shi ne yawansu ya zama daya bisa ukun kafirai, haka ma yawan makamansu da arzikinsu da yawan sojojinsu kuma sami shugaba wanda aka yi masa mubaya’a. A yau duk wadannan ka’idoji mu musulmi ba mu cika su ba.

Sai ya shawarci Gwamnati da ta kawo ayyukan da zasu sawwaka wa al’umma halin matsi da suke ciki, sannan ya hori jama’a da su maida hankali wajen neman ilimi. A karshe ya karantawa jama’a tarihin rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) da Sahabbansa kuma an yi karatun Alkur’ani da wakokin yabon Manzon Allah da kuma addu’o’in neman zama lafiya a Najeriya da ma duniya baki daya.