Zaben 2019: Matasa ba za su yi bangar siyasa ba – Sarkin Samarin Ibadan

Sarkin Samarin Ibadan Alhaji Nasiru Muhammad Yaro ya ce koka kan yadda ake amfani da matasa a matsayin ’yan bangar siyasa a lokutan zabe, inda batagarin ’yan siyasa ke bai wa matasan kayan maye su fita hayyacinsu, su tayar da hankalin jama’a. Alhaji Nasiru Yaro, ya kara da cewa a babban zabe mai zuwa ba […]

Zaben 2019: Matasa ba za su yi bangar siyasa ba – Sarkin Samarin Ibadan

Sarkin Samarin Ibadan Alhaji Nasiru Muhammad Yaro ya ce koka kan yadda ake amfani da matasa a matsayin ’yan bangar siyasa a lokutan zabe, inda batagarin ’yan siyasa ke bai wa matasan kayan maye su fita hayyacinsu, su tayar da hankalin jama’a.

Alhaji Nasiru Yaro, ya kara da cewa a babban zabe mai zuwa ba za a samu irin haka ba, domin a yanzu kan mage ya waye,  matasan kasar nan sun farga sun kuma san illar bangar siyasa domin wadanda suka yi irin hakan a baya ba su amfana da komai ba.

Ya ce “A yanzu matasanmu sun farga kowa ya mai da hankali a kan neman na kansa, ba na jin za a samu matasan da za a yi amfani da su a bangar siyasa, domin a yanzu kowa ya fahimci illar haka, matasa sun mai da hankalinsu wajen neman abin da za su rufa wa kansu asiri.”

Ya ce fadar Sarkin Samarin Ibadan ta bullo da tsare-tsare da dama domin wayar wa matasa kai tare da nusar da su muhinmmancin dogaro da kai da guje wa kayan maye, “Mun samar wa matasa da dama ayyukan yi a kamfanoni da yawa, yawancin matasanmu kan samu kansu a mummunan yanayi ne idan ba su da aikin yi, a irin haka ne za ka ga suna zaman banza da tu’ammali da kayan maye. Don haka samar wa matasa ayyukan yi hanya ce ta kyautata rayuwarsu dama kasa baki daya, domin duk al’ummar da matasanta suka zamo kintsassu masu neman na kansu wannan al’umma ta rabauta ta kuma samu tsira daga tashin hankali. Don haka muke amfani da kyakyawar alakarmu da masana’antun Jihar Oyo wajen samar wa matasanmu guraben ayyukan yi domin su zamo masu dogaro da kansu,” inji shi.

Alhaji Nasiru Yaro ya yi kira ga iyaye  su zamo masu sanya idanu a kan ’ya’yansu domin su san da su wa suke mu’amala, “Idan ka bai wa danka tarbiyya ka ba shi ilimi tamkar ka taimaki al’umma ce, domin zai ta so ya zama mai amfani ga al’umma da kasa baki daya, amma idan aka samu akasin haka sai ka haifa wa al’umma abin da zai addabe su, don haka hakkin iyaye ne su bai wa ’ya’yansu tarbiyya tare da cikakkiyar kulawa,” inji shi.

Ya ce a zaben 2019 za a samu saukin shigar matasa bangar siyasa domin yanzu rayuwa ta yi tsada kowa ya farga da neman na kansa da abin da zai rufa wa kansa asiri.