Zaben 2019: PDP ce za ta kawo Jihar Kwara- Gwamnan Kwara
Gwamnan Jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed ya bayar da tabbacin cewa Jam’iyyar PDP ce za ta lashe duk zabukan da za a gudanar a jihar. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da sabbin shugabannin jam’iyyar a ofishinsa, inda ya ce, “duba da irin mutanen da za su shugabanci jam’iyyar nan, […]

Gwamnan Jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed ya bayar da tabbacin cewa Jam’iyyar PDP ce za ta lashe duk zabukan da za a gudanar a jihar.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da sabbin shugabannin jam’iyyar a ofishinsa, inda ya ce, “duba da irin mutanen da za su shugabanci jam’iyyar nan, lallai tabbas jam’iyyar ce za ta samu nasara a zabukan da suke tafe.”