Zaben 2019: PDP na maraba da Kwankwaso
Rahotanni na nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwanso na shan matsin lamba daga wasu magoyan bayansa a kan ya koma Jam’iyyar PDP. Wata magiya ta shaida wa wakilinmu cewa “Kasancewar Kwankwaso ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani a zaben 2015 na Jam’iyyar APC, sannan yana da kima a duk fadin Najeriya, hakan […]

Rahotanni na nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwanso na shan matsin lamba daga wasu magoyan bayansa a kan ya koma Jam’iyyar PDP.
Wata magiya ta shaida wa wakilinmu cewa “Kasancewar Kwankwaso ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani a zaben 2015 na Jam’iyyar APC, sannan yana da kima a duk fadin Najeriya, hakan ya sa yake da amfani a PDP.”
Da aka tambayi Shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar ta PDP (BoT), Sanata Walid Jibril a kan lamarin, sai ya aiko da sakon waya inda ya ce “Kamar Atiku Abubakar, shi ma Kwankwaso muna maraba da shi a PDP da dukan sauran wadanda suka fice da jam’iyyar.”
Wani masoyin Kwankwaso, Alhaji Garba Gwammaja ya ce “Ina goyon bayan Kwankwaso ya koma PDP, domin bisa ga dukan alamu ba zai samu abin da yake so a APC ba. Don haka kawai ya bar jam’iyyar, kuma babu jam’iyyar da ta dace ya shiga kamar PDP.”