Zaben 2019: Sak ko cancanta?
A ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba, 2018 ne aka ayyana ta zama ranar fara gangamin siyasa da tallata jam’iyu da ‘yan takara na kakar zaben 2019. Daga jin haka, ba abin da ya zo raina illa tunawa da shekarar 2015 da ta gabata. a daidai wannan lokaci ne a wancan shekarar, jam’iyar neman canji […]
A ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba, 2018 ne aka ayyana ta zama ranar fara gangamin siyasa da tallata jam’iyu da ‘yan takara na kakar zaben 2019. Daga jin haka, ba abin da ya zo raina illa tunawa da shekarar 2015 da ta gabata. a daidai wannan lokaci ne a wancan shekarar, jam’iyar neman canji wato APC ta dauko kalmar ‘SAK’, ta wanke, ta goge ta yi wa kanta amon kirari da kwalliyar tallata ’yan takararta. A lokacin kalmar SAK a jam’iyar, tana nufin idan kana son Jam’iyar canji, ko wani dan takararta,to lallai ne sai ka nuna so ga dukkan sauran ’yan takarkar da ke cikin jam’iyar a dukkan matakai na zabe.
A takaice dai kalmar na nufin a zabi jam’iyyar a dukkan matakan zabe; hakan ya sa har suka rika yi wa kalmar kirari da “SAK daga sama har kasa”. Hakan kuwa aka yi, domin kirarin ya yi wa jam’iyar ma’ana da tasiri, abu kamar wasa sai kalmar Sak ta zama tamkar wata guguwa, a inda ta lailayo ta tashi sama da mafi yawan ’yan takarkar jam’iyar canjin, ya zame mata tamkar kwale-kwalen kai ta ga gaci a zaben 2015, domin kusan dukkan su hakarsu ta cimma ruwa (kowannensu ya ci zabe).
Sai dai wani abin da guguwar Sak ta shammaci da yawan ’yan kasa shi ne, babu wanda ya tsaya ya dubi ‘CANCANTA’, balle ya iya fayyace fa’ida ko rashin fa’idar yin Sak, domin ai tsari ne da ya hada gamayyar mai kyau da lalatacce, nagari da mugu, amma kuma duk aka rankaya aka tafi tare da nufin kawo canji. Tambayoyinmu a nan su ne:
To, shin an samu canji a sakamakon yin Sak? Ta yaya za a iya samar da canji mai kyau da inganci, irin wanda ake fata da bukata, alhalin an yi kitso da kwarkwata? Eh mana; tun da ba irin kwashi kwaraf din da guguwar canji bata dauko da niyyar su tallafa mata, don ta canza kasa zuwa ga tudun mun tsira ba. Amma ina! Ashe wasu likimo kawai suka yi don a kai su ga gaci, su ci gaba da wawure dukiyar kasa da sunan suna aiki,aka ba su cin hanci suka lale abun su, shi kuwa talaka bai ga komai a kasa ba sai musgunawa.
A baya, da an ce wa talakan kasar nan, gwamnatocin canji za su ki a kara masa albashi, ba zai taba yarda ba. A can baya, da an gaya wa talakan kasar nan ’yan majalisu za su daffare kasafin kudin kasar nan, su fifita kansu a kan bukatunsa ba zai taba yarda ba,saboda shi ya dauka Sak din da aka ce ya yi; duk da shi za ta shafa. Ya dauka su ma ’yan siyasar za su rama masa da tasu irin Sak din ne. Ya dauka su ma za su sama masa hanyoyin wadata da ababen more rayuwarsa a karkashin mukamai da wakilcin da ya zabe su don su yi masa. Sak irin nasu, ashe su kadai suke nufi.
Ko kalmar Sak da tsarinta sun samar da alfanu ga kasa kenan, ko ya abin yake? Ba wani alfanu ga jirgin Sak, domin ya sa mun yi kamun Gafiyar Baidu, ko mu ce mun yi abin nan da Bahaushe ke cewa saki na dafe. Ko sakin na hannu, kamun na guje. Watau dai an bata biyu daya ba ta gyaru ba. Mun saki cancanta, ita kuma Sak ba ta yi anfani ba.
Ina mafita? Mafita kam ita ce yin cancanta. Cancanta ita ce kalmar da ta fi kamata ga dan siyasa ya rika kirari ko takama da ita, kuma ya kasance ya ga tasirantu da ita a cikin dabi’u da kuma huldarsa ga jama’arsa, har ya kasance tana bayyana tattare da shi a halayya da zamantakewarsa da jama’a.
Ga ma’ana; ina nufin da zarar jama’a sun gan shi, za su ga cancanta a tare da shi, kyila ma su ne za su fara furta masa ita, su ce “ wane ka cancanta.”
To, mene ne cancanta da ma’anarta a siyasance? Kalmar cancanta na nufin isa da yakamata.
Babu yadda za a yi ga wanda bai isa ya yi wani abu, ya iya yin sak amar yadda ya dace, don haka dukkan lamari a rayuwa ya kasance mataki-mataki, sai wanda ka isa ka yi shi za ka iya yi,wanda kuma ba ka isa yin sa ba, sai ka bar wa wanda ya isa sai ya yi, har zuwa lokacin da kai ma ka isa yi sai ka yi. Yakamata kuwa na nufin ka isa, wani ma ya isa, dukkaninku kun isa,za ku iya yin shugabanci,wakilci ko hadimtawa jama’arku ko al’ummarku, amma kuma ai “ ba duka za a zame sarki ba”, inji Bahaushe. To ya za a yi a samu cancanta? Yadda za a yi shi ne,sai a duba dacewa. Ta yaya? Ta auna kima, mutumci, daraja, nagarta, hazaka, tausayi, jajircewa, gaskiya, amana, kishi, da sauran halaye da dabi’u na kwarai. Duk wanda aka ga nasa ya dara na dayan, to shi ne za a bai wa tutar csancanta, don ya jagoranci jama’a ko al’ummarsa.
Wannan awon shi ne jam’iyar canji ta gaza yi, sai ta yayabo Sak don ya kai ta zuwa ga gaci. Ya kai ta gacin, amma mu duba da kyau, a duk inda aka yi cancanta a tafiyar,shi ne mai kyau da tasiri. Kamar a zaben shugaban kasa, cancanta ce aka yi. Amma kuma a zabukan gwamnoni da ’yan majalisu da aka tafi a kan Sak, kalilan ne aka samu wadanda suka cancanta. Su ma a iya cewa an yi sa’a ne aka same su da cancantar tun da ba tsarinta ne ya kawo su ba, guguwar Sak ce ta hado da su.
Yau kuma, Allah Ya sake kawo mu wata kakar zabe, an fara tallata ’yan takara da jam’iyun siyasa. Babu kalar da babu (masu kirki ko cancanta da baragurbi). A don haka Sak ko cancanta wanne za mu yi?
Ni dai ina ba mu shawara da ka da mu kara yin kurma da makauniyar soyayya ga kowace jam’iya siyasa, mu natsu, mu tace, mu tantance har mu gano dan takarar da ya cancanta sai mu yi shi. Insha Allahu za mu dace da nagari.
Ya Allah ka da Ka bar mu da son mu ko zabinmu, Ka yi mana zabi mafi alheri amin.