Zaben 2019: Za a rufe kan iyakokin Najeriya
Gwamnahtin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da za a yi a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019. A wata sanarwa da Kwantirola Janar na Hukumar shige da fice ta Najeriya Mohammad Babandede, ya fitar a yau Alhamis, kamar yadda Ministan […]
Gwamnahtin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da za a yi a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019.
A wata sanarwa da Kwantirola Janar na Hukumar shige da fice ta Najeriya Mohammad Babandede, ya fitar a yau Alhamis, kamar yadda Ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriya Abdurahman Bello Dambazau ya bayar da umarni.
Dokar za ta soma aiki ne tun daga karfe 12 na ranar Juma’a 22 ga Fabrairu 2019 zuwa karfe 12 na ranar Lahadi 24 ga Fabrairu 2019.
Sanarwar ta ce, an dauki matakinne saboda a tabbatar da an yi zabe cikin lumana a fadin kasar.