Zaben 2019: Zan cika wa ‘yan Najeriya alkawari- Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a jiya Litinin ya fara kaddamar kamfen din takarar shugabancin kasa a yankin Arewa maso Yamma, inda aka gudanar a Jihar Sakkwato don bayyana wa ‘yan Najeriya matakan da zasu dauka idan jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2019. Dan takarar shugaban shugaban kasar ya bayyana wa […]

Zaben 2019: Zan cika wa ‘yan Najeriya alkawari- Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a jiya Litinin ya fara kaddamar kamfen din takarar shugabancin kasa a yankin Arewa maso Yamma, inda aka gudanar a Jihar Sakkwato don bayyana wa ‘yan Najeriya matakan da zasu dauka idan jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2019.

Dan takarar shugaban shugaban kasar ya bayyana wa dumbin masoyansa cewa, Najeriya na bukatar shugaba mai kishin gwamnati da jama’ar kasa, ba mai son kansa ba kawai kuma tana bukatar wanda zai cika alkawarin da ya daukar wa ‘yan Najeriya.