Zaben 2023: Atiku ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli

Atiku ya ce kotun baya ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke

Zaben 2023: Atiku ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli

Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya garzaya Kotun Koli domin kalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC a zaben.

A cikin karar da ya daukaka ranar Talata mai dauke da hujjoji 35, Atiku ya ce kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa karkashin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke.

Jagoran lauyoyin tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, Chris Uche, SAN, dai na rokon Kotun Kolin ne da ta jingine hukuncin kotun ta baya, saboda bai yi aiki da ainihin hujjojin da suka gabatar mata ba.

Daga ciki, Atiku ya yi zargin kotun ta tafka kuskure saboda kin soke sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, la’kari da yadda ya ce an gudanar da shi ba tare da an yi amfani da tanade-tanaden Dokar Zabe ta shekara ta 2022.

A kwanakin baya ne dai kotun sauraron kararrakin zaben ta yi watsi da bukatar Atiku da ta takwaransa na jam’iyyar LP, Peter Oni, sannan ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben.

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu