Zaben 2023: Buhari ya jefa ‘ya’yan APC a cikin duhu — Dokta Kari
Buhari ya manta da gudunmawar da aka yi masa a 2015.
A Larabar makon jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin Shugaban Kasa idan wa’adin mulkinsa ya kare.
Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da kafar talabijin ta Channels, inda ya ce “zaben 2023 ba matsalata ba ce.”
- Abin da ya sa aka tsere wa matan Hausawa a harkar kasuwanci
- Boko Haram ta sake kai hari, ta yi ta’asa a garin Chibok
Aminiya ta tattauna da masanin harkokin siyasa a Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, inda ya yi fashin baki kan abin da Shugaban Kasar yake nufi da makomar wadansu daga cikin masu zawarcin kujerarsa:
A fahimatarka me Buhari yake nufi da bai damu da wanda zai gaje shi ba?
Eh to, yana nufin abubuwa da dama, na farko yana nufin cewa ba kamar sauran shugabanni da gwamnoni da sauransu da suka dage cewa sai sun zaba wa al’umma wanda zai gaje su ba.
To mai yiwuwa shi abin da yake nufi shi ne ba zai yi hakan ba, wato ba zai tilasta kowa a kan jam’iyyarsa ba.
A baya mun ga yadda shugabanni suka yi ta fadi-tashin ganin cewa idan za su bar mulki sai sun dora ko sun kawo wani a madadinsu.
Mun ga yadda tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi ba-zata ya kawo marigayi tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa da Dokta Goodluck Ebele Jonathan.
Gwamnoni da dama sun yi haka, saboda haka, mai yiwuwa abin da Buharin yake nufi ba zai yi hakan ba, duk da yake wannan maganar ta dan yi karo da wadda ya yi a baya, a cikin hirarsa da Channels din, inda ya ce idan ma har yana da wani a zuciyarsa, ba zai bayyana shi ba, don a cewarsa idan ya bayyana shi za a iya hallaka shi ko kuma a illata shi.
Saboda haka, mai yiwuwa abin da yake nufi shi ne ba zai yi katsalandan ba, ko ba zai fito fili ya ce ga wanda yake son ya gaje shi ba.
Amma wadansu suna ganin hakan ma wata dabara ce, don zai yi wuya a ce Shugaba ya yi jagoranci na shekara takwas, yana ganin akwai wasu ayyuka kanana da manya wadanda ya yi a lokacin mulkinsa, ba zai so ganin wani ya zo ya rusa su ba ko a ce bai dora daga inda ya tsaya ba.
Saboda a halin yanzu akwai ayyuka da dama wadanda ba lallai ne ya iya kammala su kafin karewar wa’adinsa mulkinsa ba, to kuma idan ta kasance bai damu da wanda zai gaje shi ba, to wanda zai gaje shin, yana iya zuwa ko dai ya lalata wadannan ayyuka ko ya nuna halin ko-inkula ya yi watsi da su.
Wadansu ma suna ganin cewa wannan kawai dabara ce ta siyasa, wato ya fadi maganar ce saboda sauran ’yan siyasa su saki jiki, musamman ganin cewa shi tsohon soja ne, domin dama su sojoji a kullum sukan dauki komai kamar yaki ne, kuma ka san yaki dama dabara ce.
To amma idan har da gaske yake yi, abin zai yi tasiri kwarai da gaske, zai zama cewa a APC kowa tasa ta fisshe shi ke nan, wanda kuma hakan zai zafafa takarar da ake yi a wajen zaben fid-da-gwani.
Saboda haka akwai fannoni da dama da za a iya fassara maganar da Buhari ya yi.
Mene ne makomar wadanda ake tunanin Buhari zai taimaka musu idan wa’adinsa ya kare, wadanda suka rika fadi-tashin ganin ya hau mulki a shekarar 2015, misali Tinubu?
Yawwa, to, ka ga irin wadannan a halin da ake ciki ana iya cewa suna da babban kalubale, saboda a baya kasancewar suna tare da Buhari, ba ma Buhari kadai ba, duk ma wanda ya yi shugabanci, ya zama suna tare da shi ana ganin cewa suna da babbar dama ta samun nasara.
To yanzu idan ya ce babu ruwansa, kowa tasa ta fisshe shi ke nan. Ka ga su ma idan suna so su kai labari, to, dole ne su koma su sake dabara su sake shiri, kuma babban tasirin wannan shi ne zai nuna cewa, kamar Buhari ya manta gudunmawar da suka yi masa ke nan ko kuma bai saka musu ba.
Don za su rika zargin cewa bai rama wa kura aniyyarta ba.
Idan Buhari ya sauka, wane kalubale kake ganin magajinsa zai fuskanta?
Akwai kalubale da dama, don shi kansa Buhari an zabe shi ne saboda ganin abubuwa da dama sun tabarbare a kasar nan, akwai matsaloli manya da kanana da ake ganin shi Buharin zai magance.
To kuma sai aka yi rashin sa’a, yawancin wadannan matsalolin har yanzu suna nan, wadansu ma sun kara ta’azzara sun kazance, sai dai mai yiwuwa idan aka yi sa’a cikin ’yan watannin da suka rage masa, za a iya magance wasu.
Amma dai gaskiya har yanzu akwai su, musamman tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa, ba na tsammanin wani abin kirki zai canja, mai yiwuwa in har sun so su canja, za su canja, don wannan wani abu ne da yake bukatar daukar matakai kwarara.
To amma shi tattalin arzikin abin da ba a yi ba a tsawon shekara bakwai baya, ba na tunanin za a iya yin wani abu a kansa a cikin abin da bai wuce shekara daya ba.
Yaki da cin hanci da rashawa kusan yanzu ya zama a fatar baki kawai.
Akwai matsaloli manya da yawa, kamar maganar bambance-bambance da ma za a iya cewa maganar bangaranci da kabilanci da siyasa da addini kusan sun dabaibaiye siyasar Najeriya, wato sun yi ta karuwa ne a lokacin mulkin Buhari kuma ba a magance su ba.
Akwai maganar rashin aikin yi, akwai uwa-uba matsalar tsaro wadda ita ma ta kara kazancewa a lokacin mulkin Buhari, kuma ba na tsammanin za a iya samun nasara a kan Boko Haram kwata-kwata daga nan zuwa karshen mulkin Buhari, duk da yake dai za su iya cewa sun samu nasara ta wani bangaren tunda wannan matsala za a iya cewa kusan a jihohin Borno da Yobe ne kadai ta rage, sannan daga lokaci zuwa lokaci ne ake jin faruwarta a Jihar Adamawa.
Watsuwar da ta yi ya ragu, duk da dai kwanan nan an ji cewa wadansu ’yan Boko Haram suna sulalowa suna hada kai da ’yan ta’addan da suke cikin dazukan jihohin Neja da Kaduna da Zamfara da Sakkwato.
Wato dai ita wannan matsalar tsaro tana nan kuma ma sai rikidewa take yi.
Akwai rade-radin cewa Buhari zai iya bai wa Mataimakinsa Osinbajo dama ya gaje shi, kana ganin hakan zai tabbata, sannan ziyarar da tsohon Shugaban Kasa Jonathan yake kai masa a kai-a kai ba ta da wata alaka da neman wanda yake son ya gaje shi?
Ai duk wannan dai rade-radi ne, don yanzu ai sun kai mutane biyar wadanda ake cewa Buhari zai goya musu baya su gaje shi, ka ga an fito ana cewa yana da yarjejeniya da Tinubu, kuma shi kansa bai taba fitowa fili ya karyata hakan ba bare wani na kusa da shi ya karya ta.
Wadansu sun ce mukarrabansa na zawarcin tsohon Shugaba Jonathan duk da yake shi ba dan Jam’iyyar APC ba ne, wadansu sun ce yana goyon bayan Osinbajo.
A kwana-kwanan ma an fara cewa wanda yake goyon bayan ma ai Ministan Sufuri ne, Rotimi Amaechi, saboda haka wadannan rade-radi da shacifadi duk hasashe ne.
Kuma maganar da ya yi cewa ba zai fadi wanda zai gaje shi ba ko wanda zai mara wa baya ba, zai ruruta wannan rade-radi , mai yiwuwa daga nan zuwa lokacin da za a yi zaben fid-da- gwani, abubuwa za su fito fili, to amma zuwa yanzu duk abin da ake yi shaci-fadi ne kawai.