Zaben 2023: Jam’iyyun siyasa suna ci gaba da shiri

Jam’iyyar Accord ta ce nan ba da jimawa za ta gudanar da babban taronta.

Zaben 2023: Jam’iyyun siyasa suna ci gaba da shiri

Tambarin wasu jam’iyyun siyasa

Jam’iyyun siyasa a kasar nan tun daga Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar hamayya PDP sun ce sun kammala shiri domin fafatawa a zaben fid-da gwani cikin wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta kayyade.

Jadawalin zaben na 2023 ya nuna cewa jam’iyyun za su yi manyan tarukansu don zaben shugabannin jam’iyyun daga ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin bana.

Manyan tarurrukan jam’iyyun mataki ne na tunkarar babban zaben badi.

Hukumar INEC ta ce jam’iyyun da ke son shiga zaben badi a hukumance za su iya gudanar da manyan tarurrukan don zaben shugabanninsu daga ranar 4 ga Afrilu da muke ciki zuwa 3 ga watan Yuni.

Sai dai ta ce dole ne jam’iyyu su warware duk wata takaddama da kan iya tasowa sakamakon zabubbukan shugabannin cikin wata biyu da ta kebe.

Farfesa Mustapha Osuji, Daraktan Shirye-Shirye na Jam’iyyar APC, ya ce a koyaushe jam’iyyarsu na aiki da abin da doka ta ce.

“Kowace jam’iyya na da tsari game da yadda take tafiyar da harkokinta kuma Jam’iyyar APC kan duba tsare-tsaren da suka yi daidai da dokar zabe kuma za ta fitar da nata jadawali na masu son tsayawa takara tun daga majalisun jihohi zuwa na tarayya da zabbubukan gwamnonin jihohi da kuma na Shugaban Kasa,” in ji shi.

Ita ma Jam’iyyar Accord ta ce nan ba da jimawa za ta gudanar da babban taronta a matakai daban–daban.

Shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Mohammed Lawal Nalado ya ce: “A gaskiya muna cikin shiri sosai domin ya kamata mu jam’iyya mu ba da goyon baya kuma mu zage dantse mu ga cewa mun yi abubuwan da suka kamata domin a guje wa abubuwan da INEC take gudun kada su faru a gaba”.

Jam’iyya PDP ta ce za ta yi biyaya ga umarnin INEC kuma za su yi amfani da masalaha wajen fitar da ’yan takararsu a dukkan matakai.

Sai dai Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Ibrahim Abdullahi ya ce za su yi zabe a wuraren da aka kasa cim ma maslaha.

Ya ce, “Jam’iyyar PDP jam’iyya ce mai biyayya ga umarni musamman na hukumar zabe wadda ita ce ta fitar da wannan jadawali.

“Ina son in tabbatar da cewa ba mu da wata matsala, kusan jihohin da ake da matsala na mukamai muna nan muna kokarin mu yi sulhu ga ’yan takara mu ga mun fitar da yarjejeniyar a kan mutum daya.

“Idan haka bai samu ba to za mu ba da dama a yi zaben.”

Hukumar ta debar wa jam’iyyun siyasar wa’adin wata biyu don gudanar da zaben shugabanninsu da warware duk wani rikici da kan iya biyo baya.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50