Zaben Adamawa: An kasa gurfanar da Hudu Yunusa-Ari a kotu

Yunusa Ari ya yamutsa hazo bayan da ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa ana tsaka da kirga kuri’u

Zaben Adamawa: An kasa gurfanar da Hudu Yunusa-Ari a kotu

An gaza gurfanar da Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari a gaban babbar kotun jihar a yau Litinin.

Hakan ya biyo bayan gazawar ’yan sanda su sanar da Yunusa-Ari sauraron kararsa a gaban da ke zamanta Yola, hedikwatar jihar.

A cewar lauyan masu shigar da kara, Rotimi Jacobs, ’yan sandan sun kai takardar karar ta hanyar ziyartar gidansa amma a cikin takardar ba a bayyana hakikanin wanda ake tuhuma ba.

Alkalin kotun, Benjamin Manji, ya yi mamakin dalilin da ya sa ’yan sandan da suka bayar da belinsa suka gaza gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma wakilinsa.

Don haka, ya amince da bukatar lauyan masu gabatar da kara da wanda ake kara ya bayyana a gaban kotu a zama na gaba.

Daga nan ya umarci INEC ta gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba ranar 23 ga Nuwamba, 2023.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman, lauyan INEC, Rotimi Jacobs, ya tabbatar da cewa za a yi duk yiwuwa don ganin wanda ake kara ya bayyana a zama na gaba.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa INEC damar gurfanar da Yunusa-Ari wanda ke fuskantar tuhume-tuhume shida kan rawar da ya taka wajen bayyana sakamakon bogi a zaben gwamnan jihar Adamawa na 2023.

Bayan kammala zaben gwamnan a ranar 15 ga watan Afrilu, Ari da aka dakatar ya ayyana ’yar takarar APC, Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara a lokacin da ake tsaka da tattara sakamakon zaben.

Matakin nasa ya haifar da rudani, inda INEC ta yi watsi da sanarwar tare da dakatar da shi nan take.