Zaben Adamawa: Hudu Ari ya yanke jiki gabanin gurfanar da shi a kotu
An garzaya asibita da Kwamishinan Zaben Adamawa, Hudu Yunusa Ari, bayan ya yanke jiki ya fadi ana shirin zuwa gurfanar da shi a kotu
An garzaya asibita da Kwamishinan Zaben Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, bayan ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shirin zuwa gurfanar da shi a babbar kotun jihar.
Lauyanansa ya sanar da alkali a ranar Litinin cewa ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da yake shirin bayyana gaban kotu domin yi masa shari’a, kuma an garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH)
Akalla karo na uku ke nan da aka kasa gurfanar da Hudu Ari, kan zargin murde sakamakon zaben Gwaman Jihar Adamawa da kuma bayyana sakamakon bogi a yayin da ake cikin kirga kuri’u, inda ya sanar cewa ar takarar jam’iyyar APC, Aisha Binani ce ta lashe.
Daga bisani hukumar zabe (INEC) ta soke sanarwarsa aka ci gaba da kirge, wanda daga karshe aka sanar da Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP a matsayin wanda a lashe zaben.
- Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Mara Inganci Nan Take
- Rikicin Ansaru da ’yan bindiga ya sa mutanen Birnin Gwari hijira
Lauyan mai shigar da kara, Rotimi Jacobs (SAN), ya bayyana cewa wanda ake kara ya dade yana gabatar da wasiku da bukatu da dama na a jinkirta shari’ar, don haka abin da ya rage shi ne kotu ta bayar da sammacin kama shi.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Dokta Suleiman Usman (SAN), ya gabatar da rahoton likitan da aka samu daga ATBUTH a matsayin shaida na rashin lafiyar Hudu.
Dokta Suleiman ya kuma mika wata takarda daga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, wanda ya umurci kotun da ta dakatar da shari’ar Hudu na wani dan lokaci har sai an yanke hukuncin daukaka karar da ’yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Binani ta shigar a gaban kotun daukaka kara ta Abuja.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya ce Hudu babban shaida ne a shari’ar, sannan yana da muhimmanci a warware shari’ar kafin a ci gaba da gurfanar da shi.
Amma, Mai shari’a Manji ya yi watsi da wasikar kuma ya yi gargadin cewa wanda ake kara na kokarin jinkirta shari’ar kotun.
Ya kuma bukaci lauyan Hudu da ya tabbatar da cewa wanda yake karewa ya bayyana a gaban kotu domin ci gaba da sauraren karar.