Zaben Adamawa: Kotu ta kori karar da Binani ta shigar

Aisha Binani tana kalubalanar nasarar Gwamna Ahamdu Fintiri na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Adamawa.

Zaben Adamawa: Kotu ta kori karar da Binani ta shigar

Sanata A’ishatu Dahiru Binani

Babbar Koun Tarayya da ke Abuja ta kori karar da ’yar takarar Gwamnan Jihar Adamawa a Jam’iyyar APC a zaben da aka kammala, Aisha Binani, ta shigar kan zaben.

Sanata Aisha Binani ta shigar da karar kalubalanar nasarar Gwamna Ahamdu Fintiri na jam’iyyar PDP a zaben mai cike da rudani.

Ta bukaci kotun ta tabbatar da ita a matsayin zababbiyar gwamnan jihar kamar yadda kwamishinan zaben jihar da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari ya sanar da farko, ba bisa ka’ida ba.

Kafin nan, Binani ta shigar da karar neman kotun ta hana Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke sanarwar da Hudu ya yi.

Sai dai a zaman Babbar Kotun Tarayyya da ke Abuja a ranar Laraba, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya yi watsi da bukatar.

Idan za a tuna sanarwar da Hudu ya yi ba bisa ka’ida ba ta sa INEC dakatar da shi tare da umartar jami’an tsaro su bincike shi, lamarin da  ya sa ya shiga buya.

Tuni INEC ta bayyana sanarwar da ya yi alhali ana tsaka da tattara sakamakon zabe a matsayin haramtacce, ta kuma ce ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zabe.

Daga bisani bayan tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 11 da suka rage a zaben, jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele, ya sanar cewa Gwamnan Fintiri na PDP ne ya yi nasara.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos