Zaben ANA Kano: Gara Bukar da Habu
“Ba a rabu da Bukar ba wai an haifi Habu,’ inji Malam Bahaushe sarkin hikimar zance. A fahimtata da wannan muhimmin karin maganar Bahaushe yana shagube ne a duk lokacin da wani ya tsinci kansa a cikin wata matsala, amma a yayin da yake kokarin samo yadda zai kama bakin zaren, sai kwatsam igiyar ruwa […]
“Ba a rabu da Bukar ba wai an haifi Habu,’ inji Malam Bahaushe sarkin hikimar zance. A fahimtata da wannan muhimmin karin maganar Bahaushe yana shagube ne a duk lokacin da wani ya tsinci kansa a cikin wata matsala, amma a yayin da yake kokarin samo yadda zai kama bakin zaren, sai kwatsam igiyar ruwa ta sake fizgarsa cikin tekun wata matsalar.
Babu shakka, ba zan yi kuskure ba idan na ce ana kukan targade sai ga karaya ta samu a kungiyarmu ta marubuta, wadda aka fi sani da ANA Kano, musamman idan muka yi la’akari da zaben da kungiyar ta gudanar ranar Lahadi 3 ga watan Agusta, 2014.
Ba rabo da gwani ba, sannan masu iya magana sun ce, jiya ba yau ba, wato dai sai wanda ya san darajar goro shi kan adana shi a algarara, har ma ya dinga yayyafa masa ruwa. Wannan batu ga duk wanda yake bibiyar abubuwan da ke gudana a kungiyar ANA Kano ba kurman baki ba ne. Domin a iya fahimtata, a kungiyar ANA Kano ba a taba tafka kuskure irin wanda aka shirga ba a ranar Lahadin da na bayyana ba. Ai ko shakka babu, gaskiya ne cewa tsalle daya ake yi a fada rijiya, amma sai a yi dubu ba a fito ba. Kuma duk mai hankali da ya yi duba da idon basira, ya san cewa an yi kitso da kwarkwata, musamman duba da irin kunshin shugabannin da aka aura wa kungiyar a wajen wannan zabe na ranar Lahadi.
Ba zan yi kuskure ba idan na ce a kungiyar ANA Kano an yi abin nan da ake cewa gini da tubalin toka da sunan zabe.
Tirkashi! Ban taba tunanin cewa lalacewarmu ta kai matukar kurewa kamar haka ba, in ban da haka me ya kai ’yan kungiyarmu ta ANA Kano yin zaben tumun dare? Ni a iyaka sanina gada a gidan liman haramun ce, kuma ba a yin danwake da garin kwaki, domin dai shi garin kwaki in ba teba ake son kwabawa ba, a ina za a yi danwake da shi? Abin nufi a nan shi ne, a kullum idan ana son cim ma nasara a tafiya musamman ta shugabanci, to, a adalci shi ne a ajiye kwarya a gurbinta, wato dai a zabi jagororin da aka gamsu za su iya jagorancin tafiyar da za a yi, domin kayan amale ba na jaki ba ne. Idan dai ba kisan kai ake son yi ba; ba daidai ba ne a yi wa godiya gara da danyen nama, wato dai amaryar ANA Kano, a iya hangena da tunanina ba ta yi dace da sabbin shugabanni da aka aura mata ba.
Duk mai bibiyar kungiyar ANA Kano, musamman shugabancin da ya gabata, to ba zai gaza sanin sa-toka-sa-katsi tsakanin mahukuntan kungiyar da wasu mambobin kungiyar da suke kallon akwai son zuciya ko lauje cikin nadin shugabancinta ba. Kuma ko mai kushen mai kushe, idan ya lura da kunshin shugabancin jiya da na yau ya san cewa ko makaho ya san jiya ta fi yau a matakai masu yawa.
Babu shakka, shugabanin jiya suna da tasu irin gazawar, amma duk da haka, duk wanda zai fadi gaskiya cikin ’yan kungiya, ya san kunshin shugabannin jiya sun fi na yau nagarta da cancartar su yi shugabanci. Kafin na kai ga zano hujjojina, bari mu yi karatun baya kadan.
Duk da zargin da aka yi ta yi wa shugabannin jiya da kuma kokarin bata su a baya, wanda hakan ya yi kokarin yin fatali da kimarsu da kuma jefa kungiyar ANA Kano cikin kogin matsala, duk da haka zubin shugabancin yau ya gaza na dauri sau dubu. Wannan ra’ayina ne, don idan na rantse ba zan yi kaffara ba cewar zubin shugabannin da sun zarta zababbun shugabannin yanzu ilimi da cikar kamalar shugabanci har ma da kishin kungiyar a fili karara.
Kash! Rashin sani na wasu da kuma zarmewa son zuciyarsu ya kai ga suka dangwala kuri’arsu don zabar wasu wadanda a tunanina mutane ne da in ka kira su da ’yan kasuwa ba ka yi kuskure ba, don an ga zubin tafiyar da shugabancinsu a wasu kungiyoyin. Babban burinsu kawai a ce su ne shugabanni, a kullum ba su da wani buri illa yin kafafa su ne shugabanni da kuma son girma kamar gyambo, amma batun kishin kungiya ko bijiro mata da yadda za ta ci gaba, su a gurinsu batu ne wanda, da shi da shuka dusa duk daya ne. Su batun kungiya a gun su wata gada ce kawai ta kaiwa ga cim ma burinsu na son zuciya, wato dai kungiyar hanya ce da za su bi don kai ga tudun mun tsira da neman samun shiga a wasu wurare.
Bari kai tsaye na ce har gara Bukar da Habu, domin shi Bukar an san yadda ya tafiyar da shugabancin ANA Kano. Shi kadai gayya, duk wani motsi nasa ne, duk wata sanarwa daga shi ne, hadin kan kungiya kokarinsa ne. Ba shi ne shugaba ba, amma ya fi shugaban kokari da kishin kungiyar don ganin ci gabanta mai dorewa.
Babban abin takaici shi ne, yadda ’yan hana ruwa gudu masu son cim ma wasu bukatunsu na son zuciya suka kai ga tunzura zakakuri Bukar, duk da irin hakurinsa ya kasa jurewa a gudanar da zaben a kan idonsa, ya shuri takalminsa ya yi gaba. Wanda da alama hakan ce bukatar ’yan gaza gani, kuma ba kunya ba tsoron Allah suka shafa wa fuskarsu toka suka kwarmata kada a zabe shi, don ci gaba da bai wa kungiyar gudummawa, hujjarsu wai ba ya wajen don haka bai cancanci a zabe shi ba, duk da cewar tarihi ya nuna haka ta sha faruwa a baya a wannan kungiyar tamu ta ANA.
Misali na kusa, a uwar kungiya ta kasa an taba zabar Jerry Agada, wato tsohon shugaban kungiyar ANA ta kasa a matsayin mataimakin shugaban kungiyar, duk da cewar bai halarci zaman zaben ba. Irin mukamin da masu kishin ANA Kano suka so a zabi Bukar, irin sa ne aka zabi Jerry Agada duk da ba ya wajen taron, saboda sanin amfaninsa a kungiyar ya sa aka zabe shi. Amma a ANA Kano sai ’yan ina da mukami suka kekasa kasa suka ce hakan haramun ne.
Ba sai na rantse ba, kai ma/ke ma kun sani rikon kujera lamba biyu Bukar ne ya dace da rikonta in ma ban ce kujera lamba daya ba don ya yi an gani.
Me yi wa masu bin diddigi daga shekaru takwas da suka gabata (2009 zuwa yau) su ce ya haka? Ya kuma Almustapha da yake ganin baiken tsarin tafiyar da mulkin wasu shugabannin ANA Kano yanzu kuma ya dawo yana cewa su suka iya, na san za a fada sai dai zan so a gane cewa ba wai wanke wancen shugabancin na yi ba daga kuskuren da suka tabka ba, ina so ne a gane gara wancan shugabancin, domin wasu cikin masu rike da manyan kujerun sun fi na wadannan zababbun, ko ba komai a waccar tafiyar akwai kwararrun da za su iya tsayawa su yi magana gaban kowa, musamman da harshen da kasa ke amfani da shi. Ai ina jin ma uwar kungiya da harshen me jan kunne take magana don dai hakan ya kawo haduwar kan kowa ba tare da tunanin an yi son kai ba.
Wannan ke nan, wani karin gundumeman kuskure da nake ganin zai iya kawo wawakekiyar baraka ko ma ya kara tarwatsa tafiyar shi ne, yadda kiri-kiri aka hana mata iyayen giji wasu guraben kujerun tafiyar da mulkin kungiyar, duk da irin gudummawar da suke bayarwa a kungiyar ta kowacce fuska. Ba a taba yin zabe ba mata a kungiyar ANA Kano ba, yau sama da shekara goma, sai wannan karon da ’yan-ba-ni-na-iya suke son mulki. Na ga mata har a uwar kungiya ta kasa sun taka rawar gani wajen rike mukamai a cikinta. Koma dai yaya abin yake, wannan zaben ba a yi wa mata adalci ba da aka haramta musu shugabanci ko da kujera daya ce, duk da cewar su ne da mafi rinjayen kaso na marubuta littattafan Hausa a wannan jiha ta Kano. Anya ma ba irin wannan rashin adalcin ba ne ke sawa matan yunkuri samar da kungiyoyin mata zalla ba? Ba ma mata kadai ba, ba na jin mutane da ke da fatan ci gaba za su lamunci irin wannan tsarin mulkin mulaka’u, da ba ni na iya ni kadai.
Daga karshe nake jajanta wa ’yan uwa da irin wannan hali da muka samu kanmu na kakaba mana shugabannin da ba su dace su zama shugabanninmu ba, nake kuma amfani da wannan damar na bai wa Malam Bukar hakuri da mata iyayena a kan butulcin da aka yi musu. Kodayake na ji ya ce in sun yi kokari ma za a gani in ma ba su yi ba za a gani, lokaci ne kadai zai tabbar da hakan, kuma Allah Ya sa Bukar ba baki ya yi wa kungiyar ANA Kano ba, yadda za ta zama mushen gizaka, kin mace kina bai wa yaro tsoro.
Almustapha mamba ne a kungiyar ANA Kano
Za a iya samunsa a wannan adireshin imel din: [email protected] ko a wadannan lambobin: 07065717272 ko 08050983803