Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]

Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?
Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:

Da wuya a samu sahihin zabe – Musa Mutum Biyu
A.A. Masagala, a Benin

Musa Mutum Biyu: “Ina ganin wani abu ne mai wuyar gaske a ce wannan hukumar zaben da muke da ita ta iya gudanar da zabe a kasar nan kuma a karkashin wannan gwamnati mai ci ta gudanar da zabe mai sahihanci kuma al’umma a kasar nan su gamsu da sakamakonsa. Ba don komai ba ne ya sa na fadi hakan ba sai saboda ganin abubuwan da suka faru a baya na zabukan da ta gudanar a kasar nan. Ita ce ta shirya komai da karbar umarni daga sama, domin ita ainihinta ba ta talakawa ba ce saboda haka ba tana zaman kanta ba ne, suna ce kurum; ta yaudara aka rada mata don haka da mamaki a ce ta yi adalci.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu