Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?1

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]

Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?1
Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?1

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:

Ba za a iya zabe na adalci ba – dahiru Ganye
A.A. Masagala, a Benin

dahiru Hamadikko Ganye: “A matsayina na dan Najeriya, a gaskiya a yadda nake ganin al’amarin siyasa na kasar nan da matsayin ita ainihin hukumar zabe ta kasa, ta je-ki-na-yi-ki din nan, idan ta yi wa al’ummar Najeriya adalci a zaben 2015, zai bai wa kowa mamaki. Dalilina kuwa shi ne, koda a ce za ta yunkuro ta yi abin kirki, ba ta da ikon kanta a cikin wannan gwamnati saboda haka dole tana biyayya ga gwamnatin da ta kafa ta da nufin kare muradunta; wadanda ba su da amfani ga al’ummar kasa. Saboda haka, yadda aka dama ta hakan za a sha ta.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi